Hanyoyin Rage Kiba: Wane Lokaci Ne Ya Dace Ayi Motsa Jiki Domin Rage Kiba

Weight loss exercise


Wasannin motsa jiki tare da tsara chimaka su ne hanyoyin rage kiba mafiya tasiri, waÉ—anda kuma ba su da wani lahani ga jiki. Sai dai, game da motsa jiki, akwai ruÉ—ani kan wane lokaci ne mafi dacewa domin yin motsa jikin. 

Mafi yawan bincike da kuma ra'ayoyin masana kan motsa jiki na rage ƙiba sun karkata zuwa zaɓar lokacin safe kafin karyawa domin yin wannan motsa jiki na rage ƙiba, saɓanin lokutan rana ko yamma.

Daga cikin dalilan zaɓar wannan lokaci na safiya sun haɗa da cewa:

1. Idan mutum ya yi baccin awa 6 zuwa 8, to a lokacin da mutum ya tashi daga baccin kamar ya yi azumin cin abinci ne na aÆ™alla awa 6 zuwa 8. Saboda haka, yawan sugar (sinadarin gulukos) da ke cikin jininsa da safe ba shi da yawa, saboda haka, da zarar ya fara motsa jiki zai Æ™one shi. 

Bayan jiki ya ƙone ɗan ragowar sinadarin sugar na gulukos ɗin da ke cikin jini, domin cigaba da aikin motsa jikin, dole jiki ya fara tatso kitse daga sassan jiki tare da sarrafa shi da mayar da shi zuwa sinadarin gulukos domin cigaba da aikin. Shi kuwa ƙone kitse yayin motsa jiki shi ne jigon motsa jiki na rage ƙiba.

2. Hakan nan kuma, ana ganin safiya lokaci ne da ke da sauƙin ayyuka da uzurra. Mutum zai iya yin motsa jikin sa kafin fara uzurransa na ranar. Kuma lokaci ne da zai fi taimaka wa mutum ɗorewa da motsa jikin.

Sai dai, duk da haka, abu mafi tasiri wajen rage kiba shi ne jurewa da É—orewar motsa jikin akai-akai har na tsawon lokaci.

To yaushe za a fara ganin tasirin motsa jiki na rage kiba?

Motsa jiki na rage kiba na aƙalla minti 30 zuwa 60 a rana, sannan ana yi sau 3 zuwa 4 a sati, tsawon sati 6 zuwa 7, shi ne ake sa ran za a fara ganin tasirin motsa jikin. Daga ƙarshe, ka kiyayi kasadar fara atisaye ba tare da tuntuɓar kwararru ba.

Post a Comment

0 Comments