Me ke Kawo Matsalar Rashin Bacci Ga Mace Mai Ciki?


Yadda ake bacci a lokacin ciki

Rashin yin bacci a lokacin juna mace ke da ciki gaskiya ne, kuma abu ne da yawancin mata ke fuskanta. Wannan yana faruwa ne saboda haÉ—in wasu abubuwa kamar sauyin yanayin jiki, sauyin yanayin sinadaran hormones, da kuma damuwa.

Me yasa mace ke samun rashin bacci a lokacin juna biyu?

1. Yawan sinadarin hormone na progesterone yana shafar tsarin bacci na jiki. Hakanan hormones kamar estrogen da cortisol suna samun sauyi a lokacin da mace ta dauki ciki, wanda hakan na iya hana mace samun bacci mai kyau.

2. Damuwa: Yayin da cikin mace ke kara girma, yana karawa mace rashin samun kwanciyar hankali a bacci. Ciwon baya, kaikayin ƙafa, yawan fitsari da dare, da ciwon ciki ko gyambon ciki duk suna hana bacci sosai. Yawan tunani da damuwa kan yadda za a haihu, kula da jariri, halin rayuwa, da sauyin jiki su ma ba'a bar su a baya ba wajen hana mace yin bacci mai kyau.

3. Motsin Jariri: Jaririn da ke cikin ciki na iya yin motsi da dare, wanda ke farkar da mai ciki, musamman a watannin ƙarshe.

5. Wahalar Numfashi: Yayin juna biyu, mace na iya samun chushewa ko cunkoson hanci ko matsalar numfashi saboda ƙiba, girman ciki da tarin ruwa a jiki, wanda ke iya hana mace samun bacci mai zurfi.

Yadda mace za ta samu saukin rashin barci a lokacin da take da ciki 

Ana so mace mai ciki ta samu tsari na kwanciyar hankali kamin bacci, kamar yin wanka da ruwan dumi.

Mace wadda cikin ta ya fara girma ta rage shan ruwa da dare don kauce wa yawan tashi fitsari.

Yin amfani da matashin kai don tallafa wa ciki da kafa.

Gujewa amfani da waya ko kallon TV kamin bacci, da kuma shan abubuwan da ke da caffeine.

Yin dogon numfashi, yin addu'o'in bacci da tunani mai kyau kafin ki kwanta bacci.

Idan rashin baccin ya yi tsanani da yawa toh mace taje taga likita. Ki sani cewa ba ke kaÉ—ai ce ke fama da wannan matsalar rashin bacci ba, mata da yawa suna fuskantar hakan suma.


Rubutu Masu Alaƙa

1. Yadda Ake Gane Kwanciyar Jariri A Cikin Mahaifa