Meke Kawowa Jarirai Dorawar Jiki Da Idanu?

Aslm Dr Allah albarkaceni da samun haihuwa bayan mun dan samu jinkirin samun haihuwar daga baya kuma Allah swa yabamu haihuwar ÄŹa namiji bayan kwana shida da haihuwar kuma allah mai qirma ya karbe abinsa sakamakon rashin lpyr da tasa jikin yaron yayi yellow tau shi ne nake tmbya idan Allah yabamu wani wai akwai maganin da mace kesha sakamakon gudun waccan cutar

Amsa

Jariri mai dorawar idanu


Rashin lafiya wanda ke sa jariri É—orawar idanu da É—orawar jiki (Neonatal jaundice) lalura ce da ke faruwa saboda hauhawar sinadarin bilirubin a cikin jinin jarirai. 

KaÉ—an daga cikin abubuwan da ke kawo wannan matsalar su ne.

1. Rashin jituwar jinin jariri da na mahaifiyar sa (ABO incompatibility ko Rhesus incompatibility)

2. Haihuwar jariri bakwaini (premature delivery)

3. Cututtukan bakteriya da kan iya kawowa jariri sepsis

4. Rashin wasu sinadaran proteins da ke amfani a matsayin enzymes 

5. Da dai sauransu.

Toh yanzu zamu je zuwa ga tambayar ka ta cewa ko akwai wani magani da ake sha domin kare wannan matsalar idan kun ƙara samun haihuwa ? Kamin amsa wannan tambayar dole a san wane irin matsala ne ya kawowa jaririn farko wannan matsala ta ɗorawar jiki, wannan shi yasa zuwa asibiti yake da amfani.

A duk cikin abubuwan da muka lissafa masu kawo wannan matsalar ga jarirai, abu É—aya ne kawai ake iya yin allura domin kare yaran da za'a samu a nan gaba da kamuwa da matsalar neonatal jaundice, watau lalura mai sanya jarirai É—orawar jiki.

Wannan shi ne matsalar rashin jituwar jinin jariri da na mahaifiyar sa, watau Rhesus incompatibility. Matsalar Rhesus incompatibility tana faruwa ne idan mutum yana da jini Positive matar sa tana da Negative sai kuma jaririn da zasu haifa ya gado jinin babansa, watau ya zama Positive.

A irin wannan matsalar ta Rhesus incompatibility, jaririn da aka haifa na farko ya tsira, baya samun matsalar ɗorawar jiki, idan har shi ne cikin farko ga matar, amma yana iya samu idan har matar ta taɓa samun miscarriage. Jariran da za'a samu daga baya su ne zasu samu matsalar ɗorawar jiki.

Domin kare wannan matsalar akwai alluran da ake yiwa duk matar da take da jini Negative mijinta kuma Positive daga zarar ta haihu. Haka za'a yi a kowace haihuwa domin kare yaran da za'a haifa nan gaba.

Wannan shi yasa rubutun da muka yi akan gwaje-gwaje kamin aure, watau 'Premarital Screening Tests' yake da matukar muhimmanci. Bayan wannan matsala ta rashin jituwar jini ba wani magani da ake sha ko allura da ake yi domin kare wannan matsala ta É—orawar jiki.

Idan muka ɗauki naka case, bana tunanin matarka tana buƙatar wannan allurar saboda:

1. Baku je asibiti ba domin a tabbatar da cewa ga abinda ya kawowa jaririn ku É—orawar jiki.

2. Bamu san kalar jinin ka da na matar ka ba

3. Haihuwar ku ta farko ne jariri ya samu ɗorawar jiki, wanda hakan baya faruwa a Rhesus incompatibility sai dai idan mace ta taɓa samun ɓari.


Rubutu Masu AlaĆ™a 

1. Gwaje-gwajen da ya kamata ma'aurata suyi kamin su Ć™ulla niyyar aure (Premarital screening tests)  👉https://www.lafiyata.com.ng/2023/02/gwaje-gwajen-da-ya-kamata-maaurata-suyi.html?m=1