Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Gwaje-gwajen da ya kamata ma'aurata suyi kamin su ƙulla niyyar aure (Premarital screening tests)

Gabatarwa:



Aure shi ne ginshikin ginin al’umma, kuma ginshikin gina iyali da zumunci mai ɗorewa tsakanin 'yan adam.  Aure mai lafiya yana tabbatar da hana ’yan uwa kamuwa daga cututtuka na gado da cututtuka masu iya yaɗuwa daga wani mutum zuwa wani mutum ta ko wace hanya. Domin gina lafiyayyen aure da lafiyayyen iyali da kuma hana wasu cututtuka yaɗuwa, masana sun ayyana wasu gwaje-gwaje da ake kira 'Pre-marital screening tests' da ya kamata duk ma'aurata suyi kamin suyi aure.

Mene ne Premarital screening?

A harshen Hausa idan aka ce Premarital screening ana nufin tantance ma'aurata kamin suyi aure. Amma a fassarar masana Premarital screening yana nufin gwaje-gwajen da ake yiwa ma'aurata waɗanda ke kan gaɓar yin aure domin tabbatar da suna da cikakkiyar lafiyar yin aure da kuma tantancesu daga cututtukan da ake iya gado ta jini (Misali; cutar sickle cell anemia da cutar thalassemia) da kuma cututtukan dake iya yaɗuwa ta hanyar jima'i (Misali; Cutar HIV/AIDS, Cutar Sphyllis, Cutar Hepatitis B da Hepatitis C).

Gwaje-gwajen da ake yi kamin aure

A lura cewa, waɗannan gwaje-gwajen da zamu lissafa ana yinsu ne ga dukkan ma'aurata da mace da namiji. Ba mace kaɗai ake yiwa ba ko namiji kaɗai.

1. Hemoglobin genotype test (Gwajin cutar sikila)

Ya zama wajibi ga mace da mijin da zata aura su san mene ne matsayinsu a gwajin cutar sikila. Wannan gwajin shi zai sanar dasu wane irin hemoglobin suke da shi a cikin jini? Sanin wannan shi ne zai bada damar su kare kansu daga haihuwar yara masu cutar sikila. Ga yadda sakamakon yakan iya kasancewa.
  • AA + AC = Ba'a samun yara masu sikila
  • AA + SS = Ba'a samun yara masu sikila
  • AA + AA = Ba'a samun yara masu sikila
  • AA + AS = Ba'a samun yara masu sikila
  • AC + SS = Za'a iya samun yara masu sikila
  • AS + AS = Za'a iya samun yara masu sikila
  • AS + SC = Za'a iya samun yara masu sikila
  • AS + SS = Za'a iya samun yara masu sikila
  • AS + ACb = Za'a iya samun yara masu sikila
  • AS + Sβ-Thal = Za'a iya samun yara masu sikila
  • SC + SSb = Yara masu sikila kawai za'a haifa
  • SS + SS = Yara masu sikila kawai za'a haifa
Wannan jadawalin da ke sama yana nuna hemoglobin da ke jinin ma'aurata da kuma yiyuwar ko zasu samu yara masu cutar sikila bayan sunyi aure. Domin gina lafiyayyen iyali idan gwaji ya nuna za'a iya samun yara masu cutar sikila ya kyautu a fasa yin auren domin hana cutar sikila yaɗuwa da kuma kaucewa wahalar da take kawowa yara.

2. ABO blood group (Gwajin nau'in jini)

Yana da kyau ma'aurata su san wane irin nau'in jini suke da. Wannan yana da matuƙar amfani wajen gani nau'in jinin yaransu da kuma kare yaransu da wata cuta da ake kira erythroblastosis fetalis.

3. Test for Sexually transmitted infections (Gwaje-gwajen Cututtukan jima'i)

Yana da kyau idan za'a yi aure ma'aurata su tantance kawunansu daga cututtuka masu iya yaɗuwa ta hanyar jima'i domin kaucewa yaɗuwar waɗannan cututtukan. Gwaje-gwajen da ake yi sun haɗa da
  • Gwajin cutar HIV/AIDS
  • Gwajin cutar Hepatitis B da Hepatitis C
  • Gwajin cutar sanyin Sphyllis
  • Gwajin cutar HPV
  • Gwajin cutar sanyin Gonorrhoe da Chlamydia

4. Fertility test (Gwajin haihuwa)

Gwajin haihuwa yana da amfani sosai kamin ayi aure domin tantance cikakkiyar lafiyar ma'aurata a ɓangaren haihuwa. Gwaje-gwajen da za'a yi su haɗa da:
  • Namiji za'a yi mai gwajin seminal fluid analysis (SFA) kawai.
  • Mace za'a yi mata abdominopelvic ultrasound da kuma hormonal assay.

5. Test for mental health (Gwajin hankali da lafiyar ƙwaƙwalwa)

Yana da muhimmanci sosai a gwada lafiyar ƙwaƙwalwar ma'aurata domin kaucewa matsaloli da dama dake iya tasowa bayan anyi aure. Wannan gwajin zai nuna mace ko namiji suna da isasshen hankali da kuma lafiyar ƙwaƙwalwa da zasu iya jure zaman aure.

Amfanin Premarital screening

  1. Samar da lafiyayyen iyalai 
  2. Hana yaɗuwar cututtuka tsakanin ma'aurata
  3. Hana yaɗuwar wasu cututtuka da ake gado daga iyaye
  4. Kawar da zargi a tsakanin ma'aurata
  5. Tabbatarwa ma'aurata lafiyarsu
  6. Hana yaɗuwar cututtuka ta hanyar jima'i
  7. Da dai sauransu

Kammalawa

A wannan zamani yana da kyau duk ma'auratan da zasuyi aure suje ayi musu aƙalla gwaje-gwajen da muka lissafa a sama domin samun ingantacciyar rayuwar aure. Saɓanin yadda wasu suka ɗauka, ba rashin yadda da wanda zaka aura ke sa ayi gwaje-gwaje ba. Ana yin gwaje-gwaje ne domin a inganta zaman aure kuma a kaucewa aukuwar wasu matsaloli.

Idan kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake ƙasa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 

Print this post

Post a Comment

0 Comments