Gabatarwa
Mutane da yawa suna mai da hankali wajen samun karfi wajen jima’i kawai, amma ba su kula da lafiyar maniyyi (sperm) — wanda shine mafi muhimmanci idan ana batun haihuwa da Æ™arfi É—a namiji.
Masana sun gano cewa abinci yana da babban tasiri wajen ƙara lafiya da yawan ruwan maniyyi, samar da sabbin ƙwayar halittar sperm, da ma motsinsa. A cikin wannan rubutun zamu tattauna game da jerin abinci da masana suka gano cewa suna kara lafiyar maniyyi da kuma karfin da namiji a gun saduwa.
1. Kwai (Eggs)
Kwai na ɗaya daga cikin manyan abinci masu ƙara ƙwayar sperm saboda vitamin E da zinc da yake ɗauke da su.
Yana kare sperm daga lalacewa daga free radicals kuma yana taimaka masa ya motsa sosai.
2. Ayaba (Banana)
Ayaba tana Æ™unshe da vitamin B6, A, da bromelain enzyme, wanda ke taimakawa wajen sarrafa hormones masu Æ™arfafa sha’awa da Æ™wayar maniyyi.
Yana da kyau ga duk wanda ke son lafiyar sperm É—insa ya dinga amfani da ayaba.
3. Ya’yan itatuwa masu vitamin C (kamar Lemun zaki)
Vitamin C yana taimakawa wajen kare sperm daga lalacewar free radicals da kuma ƙara motsinsa (motility).
Masana sun tabbatar yana ƙara sperm count sosai idan ana sha kullum.
4. Tafarnuwa (Garlic)
Tafarnuwa na ƙunshe da allicin wanda ke ƙarfafa zagayawar jini da kare ƙwayar sperm daga lalacewa.
Yana da kyau a ci a É—an sashi cikin abinci kullum.
5. Karas (Carrot)
Karas yana da vitamin A da beta-carotene waɗanda ke taimaka wajen samar da sperm masu karko da ƙarfi.
Cin karas akai akai yana inganta motsin sperm sosai.
6. Nuts
Nuts kamar gyada, lubbatu, suna É—auke da selenium, zinc, da vitamin E – waÉ—anda ke taimaka wa Æ™wayoyin sperm su yi lafiya suna motsi sosai.
Cin su akai-akai na ƙara yawan sperm
Rubutu Mai Alaka: Ire-iren Azzakari Da Sahihan Bayanai Akan Azzakarin Namiji
No comments:
Post a Comment