Gabatarwa:
Ƙasar Hausa wadda wani lokaci ana kiranta da Masarautur Hausa, al'umma ce ta ƙananan jihohi masu zaman kansu a arewacin tsakiyar Afirka tsakanin kogin Neja da tafkin Chadi wadda ta bunƙasa tun daga karni na 15 zuwa 18. Ba a san takamaiman asalin ƙasar Hausa ba, amma wani hasashe na nuni da cewa Hausawa gungun wasu mutane ne da suka haɗu suna magana da harshe ɗaya, wato harshen Hausa. Yayin da wasu masu hasashe kuma sun bayyana kasancewar Hausawa a sakamakon hijirar da al’umma suka yi daga hamadar kudancin Sahara. Garuruwan hausawa sun sami ci gaba saboda kasuwancin gida da na yanki a cikin kayayyaki kamar gishiri, karafa masu daraja, kayan fata, da kasuwancin bayi. Da yawa daga cikin sarakuna da jiga-jigan jahohin biranen Hausawa sun karɓi Musulunci a ƙarni na 14 da na 15 miladiyya, hakan yana ɗaya daga cikin dalilan da suka sa suka sami 'yancin kai lokacin da Mujaddadi Shehu Usmanu dan Fodio ya kaddamar da yaƙin jihadi kuma ya ci yankin a farkon karni na 19 miladiyya.
Yanayi da kuma asalin ƙasar Hausa
Sunan ƙasar Hausa ya samo asali ne daga kalmar Hausa, ma'ana 'ƙasar harshen Hausa', duk da cewa yankin ya haɗa da wasu al'ummomi irin su Abzinawa, Fulani, da Zabarmawa. An fara amfani da kalmar 'Ƙasar Hausa' a karni na 16 AD, amma kamin lokacin mutane na kiran kansu bisa ga takamaiman birni ko masarautar da suka fito.
Kasar Hausa ta kasance a yankin Sahel tsakanin kogin Neja da tafkin Chadi a arewa ta tsakiyar Afirka a yau a arewacin Najeriya. Yankin Sahel yanki ne mai cike da busasshiyar ƙasa da ke gudana a faɗin Afirka tsakanin hamadar Sahara a arewa da kuma Savannah a kudu. Kasar Hausa, ta taso ne tun daga tsaunin da ake kira Air mountain a ƙasar Nijar (Arewa) zuwa jihar Filato Jos (kudu) da kuma Borno (gabas) zuwa kwarin Neja (yamma). Wannan yanki ya ga cigaban garuruwa da mutane masu magana da harshen Hausa suka yi tun daga shekara 1000 zuwa 1300 Miladiyya.
Ba a san ainihin asalin yadda garuruwan Hausawa suka haɗu ba, amma hasashen wasu masu bincike ya nuna cewa ƙasar Hausa ta haɗu ne sakamakon ƙaura da al’ummar yankin kudancin sahara suka yi, waɗanda suka yi watsi da nasu ƙasar, sakamakon ƙazantar da yankin ya yi, suka kafa sabbin matsugunai a inda ake kira ƙasar Hausa a yanzu. Wasu kuma masu bincike sun nuna cewa asalin Hausawa sun rayu ne a gabar yammacin tafkin Chadi kuma lokacin da tafkin ya yi nisa (sakamakon sauyin yanayi da ya shafi sahara) sai suka mamaye wannan sabuwar kasa mai albarka sannan daga karshe suka watsu zuwa arewa da yamma. Har yanzu, babu wata shaida ta ilimin archaeology da ta goyi bayan ɗayan waɗannan ra'ayoyin guda biyu. Sakamakon haka, akwai hasashe na uku, wato wanda ya nuna cewa Hausawa ba su yi hijira daga ko’ina ba, ’yan asalin yankin ne. Wannan hasashen ya samu goyon bayan cewa babu wani al’adar hijira a cikin tarihin Hausawa.
Duk da haka, akwai labarin wani mutum da aka kira Bayajida ko kuma Sadaukin Daura wanda ake alaƙantawa da asalin Hausawa, labarin ya samo asali ne tun ƙarni na 16 miladiyya, kuma yana nuna ƙarara tasirin Musulunci a yankin a lokacin. Bisa ga wannan labari, Bayajida, ɗan wani sarki ne daga Bagadaza, ya fara sauka ne masarautar sarkin Kanem (ko daular Bornu kamar yadda aka fi saninta a ƙarni na 16 AD). Amma masarautar kanem basuyi maraba da zuwan Bayajida ba, wanda hakan ya wuce ya nufi gabas har ya iso birnin Daura. Ko da Bayajida ya iso Daura akwai wani babban maciji da ya addabi sarauniyar garin da masarautar ta. Bayajida ya shiga ya kashe macijin nan mai tada hankali, wanda dalilin wannan jarumta yasa ya auri sarauniya. Tare da sarauniya Bayajida ya samu haihuwar ɗa namiji mai suna Bawogari. Bayajida ya ƙara samun haihuwar wani ɗa namiji mai suna Karbogari tare da wata kuyangar sa. Bawagori ɗan da Bayajida ya haifa tare sa sarauniya ya sami haihuwar 'ya'ya maza shida waɗanda kowannensu ya zama sarki a wani yanki na ƙasar Hausa. Karbogari, shi ma wanda aka haifa tare da kuyanga ya samu haihuwar 'ya'ya maza shida. Su ma waɗannan ya'yan na Karbogari sun ci gaba da mulkin wasu garuruwan Hausa guda bakwai.
Manyan Birane da Gwamnatoci
A farkon karni na 15 miladiyya da yawa kananan masarautun Hausawa sun haɗu don samar da garuruwa masu kewaye da katanga. A al'adance, akwai birane guda bakwai (wato hausa bakwai), kuma akwai wasu da basu cikin Hausa bakwai da dama. Birane masu muhimmanci sosai a ƙasar Hausa a wancan lokaci sune kamar haka: (Hausa bakwai, su ne masu alamar tauraro):
- Biram*
- Daura*
- GarunGobas
- Gobir
- Gwari
- Jukun
- Kano*
- Kebbi
- Katsina*
- Nupe
- Rano*
- Yawuri
- Yarbawa
- Zamfara
- Zaria (Zazzau)*
Kowane birni yana da sarki ko mai mulkinsa wanda watarana ake kira uban ƙasa, sarki ko uban ƙasa yana da mataimaki ko babban kansila wanda ake kira waziri, haka kuma akwai galadiman sarki da kuma karamar majalisar dattawa masu ba sarki shawara - yawanci majalisar ta kan ƙunshi membobi tara waɗanda kuma su ke da alhakin tantance wanda zai gaji sarki. Sarki ya kan naɗa jami’ai daban-daban, alal misali, mai karbar haraji, mai jagorantar rundunonin sojoji na birnin, da tabbatar da tsaro a kan tituna, da mai kula da amfanin gona (sarkin noma). Babban gari yakan yi mulkin sauran ƙananan masarautu ko ƙauyuka da ke kusa da shi, tare da naɗa musu msi shugabantar su a matsayin Hakimin gari.
Al’ummar Hausawa na karkara manoma ne da suke yin aikin gona na al’umma gaba daya. Bayan wani tsawon lokaci, yayin da wasu birane suka zama masu zaman kansu, wannan tsarin ya lalace ta hanyar sarakuna suna ba da filaye a matsayin kyauta ga wasu mutane. Daga hakan sai noma ya koma cin gashin kai, kowa sai ya noma abinda zai yi amfani dashi sannan ya sayar da ragowar.
0 Comments