Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Hanyoyin Kiyaye Basir Mai Tsiro Cikin Sauƙi

Gabatarwa

Basir mai tsiro wanda ake kira da "hemorrhoids" ko kuma "piles" a turance, lalura ce da ke ci gaba da shan gurguwar fahimta a tsakanin al'ummar Hausawa.

A likitance, ba wani abu ne ake kira basir ba face kumburar jijiyoyin jini a cikin ƙarshen babban hanji da kuma dubura. Waɗannan kumburarrun jijiyoyin jini su ne suke talewa har su yi bulli cikin ƙarshen babban hanji ko kewayen dubura. Basir a cikin ƙarshen babban hanji shi ne "basir cikin dubura wanda aka fi sani da internal hemorrhoid a turance" yayin da basir a kewayen dubura shi ne "basir wajen dubura ko kuma external hemorrhoid a turance"(1). 

Haka nan, "basir mai tsiro" ci gaban "basir cikin dubura" ne wanda ke bayyana yayin da  matsalar ta je matakin ƙarshe. "Basir mai tsiro" na faruwa ne sakamakon zazzagowa ko saukowar jijiyoyin jinin da suka yi kumbura sukayi bulli zuwa wajen dubura, musamman yayin yunƙuri(1).

Alamomin Basir

Bayyanar alamomin basir ya danganta ga wane irin basir ne ya bayyana, "basir cikin dubura" ko kuma "basir wajen dubura".

Alamomin basir na cikin dubura

1. Zubar jini ba tare da jin ciwo ba yayin banhaya

2. Basir mai tsiro wanda ke fitowa wajen dubura har sai an tura da yatsa domin mayar da shi. Yana haifar da ciwo da raɗaɗi da kuma zubar jini(2).

Alamomin basir wajen dubura

1. Ciwo mai raɗaɗi

2. Ƙaiƙayi 

3. Kumburi a kewayen dubura

4. Zubar jini yayin yunƙurin banhaya.

Me ke kawo basir?

Har ila wayau masana ilmin likitanci basu gane takamaiman abinda ke kawo basir ko dankanoma ba, amma duk da haka ana alakanta shi da gado da kuma wasu abubuwa(2).

Basir na faruwa sakamakon takura jijiyoyin jini a dubura har su kumbura sannan su yi bulli saboda abubuwa kamar haka:

1. Yawan yunƙuri lokacin banhaya.

2. Tsawaitar lokacin banhaya.

3. Fama da atini ko kuma 

4. Yawan yin bayan gida mai tauri na tsawon lokaci.

5. Kasancewa mai Ƙiba ko kuma teɓa.

6. Kasancewa mai juna biyu.

7. Cin abincin mai ƙarancin dusa, harza ko ganyayyaki.

8. Ɗaga kayan nauyi akai-akai.

Hanyoyin Kiyaye Basir ko Dankanoma Cikin Sauƙi

Hanya mafi kyau wajen kiyaye kai daga basir ita ce sanya bayan gida ya zamo mai taushi yadda zai iya ficewa ba tare da yunƙuri sosai ba.

Waɗannan hanyoyi za su taimaka wajen kiyaye kai daga basir ko dankanoma da kuma rage matsalolinsa(2):

1. Cin abinci mai sinadaran fiber sosai: Abinci mai sinadaran fiber sun haɗa da 'ya'yan itatuwa, ganyayyaki da kuma tsabar hatsi.

2. Shan isashshen abinsha: Shan isashshen ruwa aƙalla lita biyu zuwa uku kowace rana da sauran ababen sha masu ruwa-ruwa kamar su kankana, lemu mai bawo, ayaba da dai sauransu.

3. Rage yunƙuri yayin banhaya: Yunƙuri tare da riƙe numfashi yayin banhaya na takura jijiyoyin jini a cikin babban hanji da dubura.

4. Garzayawa da zarar an ji bayan gida: Yin buris da bayan gida yayin da aka ji shi na janyo bayan gida yayi tauri, saboda hanji zai ci gaba da tsotse ruwan bayan gidan har ya yi tauri.

5. Kula da yin atisaye: Atisaye ko motsa jiki na taimakawa rage taurin bayan gida. Haka nan, atisaye na taimakawa wajen rage ƙiba wanda hakan zai rage nauyi ko takura ga jijiyoyin jini a cikin dubura.

6. Kaucewa dogon zama ko tsugunni: Dogon zama musamman yayin banhaya na ƙara takura jijiyoyin jini a dubura.

Kammalawa

Basir ko dankanoma larura ce da ake iya samun waraka bayan amfani da magunguna da sauran hanyoyi a likitance. Amma idan basir ya yi tsanani yin tiyata na iya zama tilas. Domin sanin yadda ake maganin basir ko dankanoma mai tsiro, ku karanta da mukayi wanda shi ne bakandamiya game da yadda ake maganin basir a likanci 

Yana da kyau a tuntuɓi likita da zarar alamomin basir sun bayyana a gareka maimakon shan magungunan gargajiya da ba ka da tabbacin ingancin su.

Idan mai kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake ƙasa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 

Nassoshi


Print this post

Post a Comment

0 Comments