Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Canje canjen yanayi da ke faruwa ga mata a lokacin jinin al'ada

Gabatarwa

A farkon watan Mayu na shekarar da ta gabata, kasar Spain ta samar da wata doka da za ta bayar da hutu ga mata ma'aikata da ke faÉ—awa mawuyacin hali lokacin da suke jinin al'ada.
Daftarin dokar ya bayyana cewa za a iya bai wa mace hutun kwana uku a duk wata, kuma ana iya tsawaitawa zuwa kwana biyar a wasu lokuta idan ta bukaci hakan(1).

Premenstrual Syndrome (PMS) kalma ce da likitoci ke amfani da ita wajen bayyana wasu canje-canjen halaye da kuma yanayi da ke faruwa ga mace a lokacin da take daf da fara yin jinin al'ada ko kuma bayan ta fara. Masana sun Æ™iyasta cewa kashi 75 cikin 100 na mata suna fuskantar wasu daga cikin alamomin Premenstrual Syndrome a lokacin da zasu ga jinin al'ada ko kuma bayan sun fara a kowane wata(1). 



Alamomin ba suna faruwa bane sakamakon wani ciwo ko rashin lafiya, suna faruwa ne sakamakon sauye-sauyen wasu sinadaran hormones a cikin jinin mace da ke faruwa sanadiyyar zuwan jinin al'ada. Amma duk da haka alamomin premenstrual syndromes sukan iya tsananta ga wasu mata har su hana su  sukuni da iya yin aikin yau da kullum wasu ma har su wajabta musu ganin likita(2).

 Alamomin canje-canjen da ke faruwa a lokacin jinin al'ada

KaÉ—an daga cikin alamomin da wasu mata ke fuskanta a lokacin da suke daf da fara yin jinin al'ada ko bayan sun fara, sun kunshi wadannan(1):

  • Mafi yawancin mata sukan sami ciwon mara. Ciwon yana faruwa ne sakamakon takura da mammatsewar tsokokin mahaifa domin su turo jinin al'ada a waje. Wannan ciwon yakan tsananta ga wasu mata sosai. Ba raggwantaka ba ce idan mace ta yi kuka a wannan yanayin, saboda tsananin ciwon kan haddasa takura sosai. Domin karin bayani game da wannan ciwon da kuma yadda ake maganin sa, ku karanta wannan rubutun da mukayi a baya; "Ciwon mara a lokacin jinin al'ada da kuma yadda ake maganin sa".
  • Mafi yawancin mata suna shiga wani yanayi na Æ™unci da É“acin rai ba gaira ba dalili, ko jin haushin na kusa da su a lokacin da suke yin jinin al'ada, al'amarin da aka fi sani da mood swing a turance. Mood swings yana faruwa ga mata a lokuta dayawa amma yafi faruwa a lokacin jinin al'ada saboda wasu dalilai. Dalili na farko wanda kuma shi ne babban abinda ke kawo mood swings, shi ne sauye-sauyen sinadaran hormones dake faruwa a jikin mace a lokacin da take yin al'ada musamman Æ™arancin sinadarin hormone na Serotonin. Wannan hormone na serotonin a turance anayi masa laÆ™abi da "Happy hormone" watau ma'ana sinadarin hormone mai sanya farin ciki. Rashin daidaituwar wannan sinadarin hormone na serotonin shi yake haifar da mood swings, idan yayi karanci sai yasa mutum jin É“acin rai ba dalili, idan yayi yawa sai yasa jin farin ciki. Ƙarancin wannan hormone dake faruwa yayin jinin al'ada shi ne jigo cikin manyan dalilan da da ke sa mata suna jin É“acin rai ba gaira ba dalili yayin da suke yin al'ada. Sauran dalilan da kan iya sa mace É“acin rai a wannan lokaci sun haÉ—a da ciwon mara wanda mukayi bayani a baya, rashin jindadi ko kuma ciwon nono marar tsanani da kuma sauran alamomi da mata ke fuskanta yayin al'ada da zamu ambata a nan gaba. A lura cewa mood swings yana faruwa ba dole sai a lokacin al'ada ba, mata sukan iya samun mood swings lokaci bayan lokaci. Haka kuma, mood swings ba yana sa É“acin rai ko baÆ™in ciki kawai ba, watarana yana sa mata farin ciki da jindadi ba gaira ba dalili.
  • Wasu matan sukan fuskanci matsanancin ciwon baya, da ya kan iya hana su zama sai dai kwanciya kawai.
  • Wasu sukan fuskanci ciwon gaÉ“É“ai, wanda hakan na iya saukar musu da kasala da rashin kuzari.
  • Wasu na fuskantar matsanancin ciwon kai, da zazzabi, wasu matan kan samu tashin zuciya da amai.
  • Wasu ma kan yi amai da gudawa, ko kuma gudawar gabanin lokacin jinin al'ada ko kuma bayan sun kammala.
  • Wasu kuma abin ya kan zo musu da yawan bacci da kasala, duk inda suka samu sai kwanciya.
  • Wasu kuma tashin zuciya da É—an kwaÉ—ayi-kwaÉ—ayi suke fama da shi kamar irin na masu ciki.
  • Wasu kuma suna jin ciwon nono marar tsanani ko rashin jin dadi a nonuwansu ko kuma suji kamar nononsu ya cika ko ya kumbura.

Mene ne magani?

Idan har mace tana shiga cikin mawuyacin hali sakamakon sauye-sauyen da ke faruwa a lokacin da take cikin wannan lokaci toh zata iya amfani da magungunan rage raɗaɗi da ciwo dangin NSAIDS domin rage ciwon mara da sauron ciwon gaɓɓai. Haka kuma za ta iya yakar ƙunci da ɓacin rai ta hanyar yin abubuwan da suke ba ta nishadi a baya, kamar karatun littafan novels ko kuma kallon finafinai da wasannin kwaikwayo masu sanya nishaɗi. Amma duk da haka wasu mata sukan shiga cikin yanayin kunci mai tsanani wanda har yakan iya sa su kamu da ciwon damuwa (depression), idan har mace ta lura da haka to ya kamata ta garzaya asibiti domin ganin likita(2).

Kammalawa

Wadannan alamomi da kuma sauye-sauyen, suna faruwa ne a lokacin da mace ke yin jinin al'ada ko kuma daf da tana batun farawa, haka kuma sunfi tsanani a kwanakin farko. Bugu da kari, alamomin suna dainawa kafin mace ta gama ko kuma kwanaki kadan bayan tayi tsarki.

Idan mai kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake Æ™asa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 

Nassoshi


Print this post

Post a Comment

0 Comments