Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene ne Ingancin Gwajin Ciki Da Gishiri?

Gwajin ciki da gishiri ɗaya ne daga cikin gwaje-gwajen ciki na gargajiya da mutanen daa ke amfani da shi domin gane mace mai ciki. Yayin da wasu masu rubutun ra'ayi a yanar gizo da YouTubers suke rantsewa cewa sakamakon gwajin daidai ne, kwararrun likitocin ba su yarda da hakan ba.

Gwajin ciki da gishiri baya da inganci a tsarin ilmin kimiyya da fasaha na yanzu saboda baya da tushe ko asali, kuma sakamakon sa na da rikitarwa.

Har ila wa yau babu binciken kimiyya da fasaha da ya iya tabbatar da ingancin gwajin ciki da gishiri, sai dai an bar shi ne a matsayin gwajin gargajiya ne kawai da mutanen dori su ke yin amfani da shi domin gane wadan da suke da ciki.

Yadda Ake Gwajin Ciki Da Gishiri 


Gwajin ciki da gishiri, gwajin ciki ne wanda ke buƙatar sinadarai biyu:
  • Gishiri da fitsarin mace
Ana buƙatar fitsarin mace wanda take yi daga tashin ta daga bacci da safe, ma'ana fitsarin da ya kwana a cikin marar ta.

Wannan fitsarin na tun da safe za'a yi shi ne a cikin kwano ko kofi ko buta, sannan a samu gishiri kimanin cokali uku a zuba a cikin kwanon da fitsarin yake a ciki.

Daga nan kuma za'a bar fitsarin da gishirin su garwaye a cikin kofin na tsawon kimanin sa'o'i 6 zuwa 8.

Magoya bayan gwajin sun yi iƙirarin cewa idan mace na da juna biyu, gishirin zai garwaye da wani sinadarin hormone da ake kira human chorionic gonadotropin (hCG), wanda ake samu a cikin jini da fitsarin mata masu juna biyu. Wannan garwayewa zai sa fitsarin yayi kumfa.Amma kuma idan mace ba ta da ciki, toh fitsarin ba zai garwaye da komai ba, saboda haka ba wani kumfa da zai tashi a saman kofin.

Toh abin lura a nan shi ne, hakika gaskiya ne ana samun wannan sinadarin hormone na human chorionic gonadotropin (HCG) a cikin fitsari da jinin duka wata mace mai juna biyu amma binciken kimiyya da fasaha bai tabbatar da wannan sinadarin hormone yana iya garwayewa da gishiri ba, balle har ya bada kumfa.

Kammalawa

Duk da cewa gwajin ciki da gishiri zai iya zama gaskiya ga wadanda suka yi imani dashi, amma yana da kyau mutane su gane gwajin ciki da gishiri baya da wani tushe a ilimin kimiyya na zamani, baya da inganci, kuma sakamakon sa yakan iya zama mai rikitarwa.

Akwai aƙalumman gwajin ciki masu inganci da tushe a ilimin kimiyya da fasaha wadanda sakamakon su ke da saukin ganewa, kuma zaku iya amfani dasu a gida ta hanyar amfani da fitsarin mace. Zaku iya samun wadannan alƙalumma a sauƙaƙe a shagunan magani mafi kusa da ku.

Print this post

Post a Comment

0 Comments