Abubuwan Da Ke Iya Hana Mace Daukar Ciki Bayan Aure

Me ke hana mace daukar ciki


Samun ciki abu ne wanda mafi yawancin ma’aurata ke fara nema daga zarar an daura aure. A wani lokaci ana samun matsalar rashin samun ciki da wuri kuma wannan ya na kawo matsaloli da tashin hankali tsakanin ma’aurata.

Matsalar rashin daukar ciki na iya kasancewa daga bangaren amarya ko angon. Ma’ana ba duk rashin daukar ciki ke zama matsalar mace kaÉ—ai ba.

A cikin wannan rubutu zamu yi bayani game da matsalolin mata da ke iya hana mace daukar ciki bayan ta yi aure tare da samun isasshen saduwa da mijinta.

1. Rikicin Jinin Haila

Idan mace ta kasance tun farko jinin al’adar ta ba ya zuwa a lokacin da ya kamata ko kuma ta iya wata uku ko huÉ—u ba tare da ganin jinin al’ada ko period dinta ba, toh wannan na iya sa ta samu rashin daukar ciki da sauri. 

Wannan matsala ta rikicin jinin haila tana buƙatar zuwa asibiti domin ayiwa mace gwaje-gwajen jini domin duba yawan sinadaran hormones da ke a cikin jinin ta. Wannan matsalar ana iya shawo kanta da ikon Allah.

2. Yawan Shekaru Ko Tsufa 

Daukar cikin farko bayan 'ya mace ta haura shekaru talatin na iya zuwa da wasu matsaloli kamar zubewar ciki da haihuwar yaro mai wata naÆ™asa. A lokacin da mace ta ke da shekaru 17 ko abin da yayi sama amma ba ta kai shekaru talatin ba toh tafi samun ciki mai lafiya a gamin farko. Domin tana da cikakkar lafiyar samun juna biyu a cikin sauki. 

Haka kuma mace na kara shekaru, inganci da yawan ƙwayoyin halittar dactaje samarwa yana kara raguwa a kowane wata.

3. Matsalar Endometriosis

Rashin lafiya ne ko ciwo wanda ke iya sa wani bangaren mahaifa yayi kauri da Æ™arfi ta yanda zai hana Æ™wan namiji da Æ™wan mace su haÉ—u. Kuma hakan ya iya hana daukar ciki  ga mace. Ana iya gano wannan matsala kuma a magance ta a asibiti.

4. Kiba mai yawa ko rama mai yawa 

Idan mace ta na da kiba sosai ko kuma mace tana da rama sosai wannan yana iya hana mace daukar ciki da wuri saboda yawan kiba ko rama yanada tasiri sosai ga sinadaran hormones na jinin mutum, so yawan kiba ko rama zai iya kawo rashin daidaituwar sinadaran hormones na haihuwa a jikin mace. Akwai gwaje-gwajen da ake iya yi a asibiti kuma a bada shawarwari ko maganin da zai taimakawa mace.

5. Rashin Ni’ima

Bushewar gaban mace ko rashin samar da isasshen ruwan ni'ima daga bakin mahaifa, na iya hana ƙwan namiji samun sukunin shiga mahaifa bayan saduwa. Wannan ya na iya hana mace daukar ciki da wuri.

6. Infection Ko Ciwon Sanyin Mata

Akwai mata da dama masu fama da ciwon sanyin mata, kamar sanyin PID, amma basa shan magani akan Æ™a’ida. A irin wannan halin infection din na iya mamaye mahaifa ko kuma ya mamaye maran mace kuma ya hana ta daukar ciki ta hanyar toshe bututun fallopian, wanda a cikin sa Æ™wan namiji ke haduwa da na mace domin daukar ciki.

7. Matsalolin Mahaifa

Matsalolin mahaifa da ake haihuwar mace dasu ko waÉ—anda mace zata iya samu bayan ta balaga kamar irin su kullutun fibroid, uterine synechiae da dai sauransu duk zasu iya hana mace daukar ciki da wuri. Ko su hana ta samun haihuwa baki daya, ya danganta da wace irin matsala ce.

8. Rashin Daidaituwar Sinadaran Hormones 

Rashin daidaito na sinadaran a jikin mace kamar sinadaran sex hormones, sinadaran thyroid duk suna iya hanawa mace daukar ciki da wuri.

9. Magani 

Amfani da wasu magunguna barkatai ba bisa tsarin likita ba yana sa mace tayi jinkiri wajen samun ciki idan tayi aure. Kamar magungunan hana daukar ciki da bada tazarar iyali, musamman waÉ—anda ake yin allura. Allurar bada tazara iyali tana da wannan matsalar wani lokaci, idan mutum yayi ya daina toh zai iya shan wahala kamin samun ciki.

Haka kuma amfani da miyagun kwayoyin shaye-shaye masu sa mutum marisa, ko shan sigari, ko mata masu shan giya, wadannan da suna iya samun jinkirin samun ciki duk da cewa suna samun kyakkyawar kulawa a gefen saduwa.