Alamomin Cutar Prostate ta BPH da Yadda ake Maganin ta

Maganin girman prostate


Ita wannan prostate din wata gland ce dake kewaye da kwararon bututun azzakarin namiji daga can ciki wajen karshen tushen azzakari. Tana da ayuka dayawa, kadan daga cikin ayukan ta akwai:

1. Sarrafa fitar fitsari:- Gland din prostate ita ke matse kwararon azzakarin namiji daga can ƙarshe ta ciki ta yada fitsari ba zai zo ma ba sai ka sake ta sannan take sakin bakin kwararon zakari sai fitsari ya fito.

Maganin cutar prostate


2. Ita ke samar da ruwa mai kauri da ke fitowa tare da Æ´aÆ´an maniyyi a lokacin saduwa.

Duk lokacin da mutum yakasance baya motsa jiki, baya yawan saduwa da matar sa ko matan sa, ana samun rashin daidaiton Hormones din TESTOSTERONE da ESTROGEN, sai sinadarin ESTROGEN ya rinjaye TESTOSTERONE sai wannan prostate din tayi reacting da wannan ESTROGEN din sai ta kumbura ta toshe bakin mafitsara daga ciki.

Alamomin Cutar Prostate na BPH

Alamomin cutar prostate suna farawa ne sannu sannu har sukai wani matakin da sai anyi ma mutum aikin tiyata. Alamomin sun haÉ—a kamar haka;

1. Mutum zai ga fitsarin sa ya rage fita da karfi, ma'ana kana jin fitsari amma ya riƙa fita kaɗan kaɗan ba karfi har ya kare, kuma da yawan lokuta baka iya gama fitsarin yake daina zuwa.

2. Wani lokacin sai kafi mintuna 2 ko 3 kana fitsari, amma sai ka miƙe tsaye sai wani yazo ya ɓata ma wando. Ba sanyi bane, kamar yadda masu tallar maganin sanyi ke fada, cutar prostate na BPH ne.

3. Karancin ruwan maniyyi yayin da mutum ke saduwa da iyalan shi

4. Wani lokacin mutum infection din prostate yake fama dashi, sai infection din yasa Prostate din ta kumbura, amma still zai ji irin wadancan alamomin kamar, fitar fitsari kaÉ—an-kaÉ—an, ragowar fitsari, mutum ya gama fitsari amma yaji kamar akwai saura, karancin ruwan maniyyi da dai sauran su.

5. Idan abun yayi nisa, zai toshe bakin kwararon azzakarin daga ciki yakasance mutum baya iya fitsari kwata-kwata sai an saka masa robar fitsari (catheter) ko anyi wani abun da ake kira SPA (supra pubic aspiration) idan catheter din taki wucewa a cikin kwararon azzakarin shi.

Yadda ake Maganin Cutar Prostate 

1. Kayi ƙoƙarin zuwa ganin likita a duk lokacin da kaji wani canji ko wata matsala a jikin ka. Kada ka tsaya sayen maganin sanyi da basir, da yawan su anti-inflammatory drugs ne suke jiƙawa su sayar ma, kaji sauki ba kaje asibiti ba sai lokaci ya kure ma.

2. Ka rika yin motsa jiki iya gwargwado da kuma saduwar aure da matar ka Aƙalla sau 2 ko 3 a sati ko fiye da haka.

3. Yawan motsa jiki ko exercises kullum, yana magance 95% na matsalolin jiki.

4. Idan baka da aure har ka kai shekaru 35 ka riƙa yin exercise yana hana kamuwa da wannan cutar.

6. Idan kana da aure amma kana wani gari kana aiki baka tare da matar ka, ka rika exercise yana keeping din Hormones dinka BALANCED ta yanda ba zaka kamu da wannan matsalar ba.


Rubutu Masu AlaÆ™a 

1. Fitar Farin Ruwa Mai Kauri Daga Gaban Namiji 

2. Bayani Game Da Tsukewar Bututun Fitsari (Urethral stricture)

3. Ire-iren Azzakari Da Sahihan Bayanai Akan Azzakarin Namiji

4. Bayani Game Da Karkacewa Ko Lankwasher Azzakarin Namiji

5. Yadda Ake Tsokano Sha'awar Namiji Zuwa Kwanciyar Aure