Gabatarwa
Shigar ciki wani babban canji ne a rayuwar mace, kuma yana zuwa da sauye-sauye na jiki da hankali. Mata da dama kan fara jin sauyi tun cikin makonni na farko na daukar ciki, koda ba su kai lokacin jinkirin al’ada ba. Wannan yasa tambayar “alamomin shigar ciki a satin farko” ke zama daya daga cikin abubuwan da ake yawan bincike a shafin intanet.
A cikin wannan cikakken bayani, za mu tattauna:
- Alamomin farko na shigar ciki
- Banbanci da sauran cututtuka
- Lokacin da ya dace a yi gwaji
- Abubuwan da ke tayar da rudani
- Shawarwarin lafiya da ya kamata ki bi
Me Ke Faruwa a Satin Farko na Shigar Ciki?
Da zarar maniyyin namiji (sperm) ya haÉ—u da kwai (egg) a lokacin ovulation, ciki zai iya shigar mace. A irin wannan lokaci:
- Kwai É—in da aka kyankyashe da maniyyin namiji yana kama hanya zuwa kogon mahaifa (womb).
- Ana samun implantation (inda kwan da ke dauke da maniyyi ya nutse a cikin bangon mahaifa).
- Jikin mace zai fara fitar da sinadarin hormone na hCG (human chorionic gonadotropin) wanda ke nuna alamar shigar ciki.
Wadannan canje-canje suna farawa ne tun shigar ciki a satin farko, koda kafin mace ta gane ta samu jinkirin al’ada.
Manyan Alamomin Shigar Ciki a Satin Farko
1. Karamin Ciwon Mara ko Zafin Ciki
Wasu mata na jin karamin ciwon mara da takura kaÉ—an, wanda ke kama da ciwon mara na lokacin al'ada. Wannan yana iya zama alamar implantation. Implantation shi ne nutsewar ciki a bangon mahaifa, shi ne ke haifar da ciwon mara a lokacin shigar ciki.
2. Fitar Farin Ruwa daga Gaban Mace
Fitar ruwan farji mai laushi, fari ko ɗan rawaya na iya faruwa. Wannan yana da alaƙa da ƙaruwa sinadaran hormones.
3. Gajiya Da Kasala
Jikin mace yana fuskantar gajiya sosai tun satin farko. Yana yiwuwa mace ta kasa yin abubuwan yau da kullum saboda sauye-sauyen sinadaran hormones da take samu a jikin ta. Wannan shi ke haifar da gajiya a farkon shigar ciki.
4. Jin Nishi Da Wahala
Wasu mata na iya jin sanyi ko nauyi a kirji, wanda wani lokaci na shafar numfashi.
5. Tashin Zuciya Da Amai (Morning Sickness)
Ko da yake ba kowa ke fuskantar shi ba a satin farko, wasu na iya fara jin tashin zuciya da amai da zarar cikin ya kama. Shi ma amai da tashin zuciya a farkon ciki yana faruwa ne saboda ƙaruwar sinadaran hormones na ciki.
6. Jin DaÉ—in Barci Fiye da Kima
Hormone na progesterone yana haifar da barci mai nauyi ko yawan barci fiye da yadda aka saba. Wannan sinadarin kuma yana ƙaruwa sosai a farkon ciki.
7. Damuwa
Sauye-sauyen hormone na iya haifar da damuwa, rashin kwanciyar hankali, ko jin bakin ciki ba gaira ba dalili.
8. Jin Ciki Yana Cika Ko Ƙoshi ba Tare da cin Abinci ba
Wasu mata na jin cikinsu ya cika ko kumbura, kamar suna da iskar ciki – wannan yana da alaÆ™a da sauyin sinadaran hormones na mace
9. Sauyin Launin Nonon Mac
Launin kasan kan nonon mace (areola) yana iya fara ɗan duhu ko kumbura fiye da yadda aka saba gani. Nono na canza launi a lokacin ciki, ƙasan kan yakan yi duhu, kuma ba zai koma yadda yake ba har abada.
10. Jin Ƙaiƙayi Ko Zafi a Nono
Haka kuma wani lokaci nono yakan dan kumbura ya fara yiwa mace zafi, kamar ciwon nono ko nauyin da ke kawo rashin jin daÉ—i – wannan yana É—aya daga cikin farkon alamomi na shigar ciki.
Alamomin Shigar Ciki Masu Kama da Cututtuka Ko Al’ada
Wasu daga cikin alamomin shigar ciki a satin farko suna kama da na al’ada (menstruation) ko ciwon ciki kamar irin su:
- Ciwon mara mai laushi
- Jin nauyi a ƙirji
- Ƙuruciya daga farji
- Gajiya
- Jin zafin ƙirji (heartburn)
Saboda haka yana da wuya a tabbatar da ciki har sai an yi gwajin ciki.
Yaushe Ya Kamata A Yi Gwajin Ciki?
Kodayake akwai alamomin ciki tun kafin jinkirin al’ada, mafi kyawun lokaci na yin gwajin ciki shine kwana 7 zuwa 10 bayan mace ta samu jinkirin al’ada.
Hanyoyin Gano Ciki:
- Gwajin fitsari na gida (home pregnancy test)
- Gwajin jini a asibiti
- Ultrasound (idan an kai makonni 5 zuwa sama)
Alamomin Shigar Ciki Da Ba Kowa Ke Fuskanta Ba
- Jin wari ko ƙamshi fiye da kima
- Jin ɗaci ko canjin dandano fiye da ƙima
- Ƙaiƙayi a fata
- Jin kumburi a ƙafa ko hannu (ba safai yakan faru ba)
Abubuwan Da Ke Iya RuÉ—ar Da Ke Cewa Kina Da Ciki
Wasu alamomin na iya zuwa ne ba don ciki ba. Misali:
- Ciwon mara Al’ada na gabatowa
- Fitar farin ruwa daga farji na Infection ko hormones
- Gajiya Rashin bacci, damuwa ko cin abinci mara kyau
- Jin É—aci a baki Cututtuka ko magunguna
- Jin ƙaiƙayi a nono na Canjin hormonal ko PMS
Yadda Zaki Kula da Kanki Idan Kina Zargin Shigar Ciki
- Gujewa shan magani ba tare da shawarar likita ba
- Ci abinci mai lafiya (protein, fruits da ganye)
- Cin abinci mai kyau ga mai juna biyu
- Guji shan giya, shan taba, da caffeine da yawa
- Yawaita shan ruwa
- Rage gajiya da damuwa
Shawarwari Ga Budurwa Da Take Zargin Shigar Ciki
- Idan kina da shakku ko damuwa, ki tuntubi likita ko asibiti mafi kusa.
- Kada ki shiga damuwa ko jin kunya – lafiya da amincewa da kai sune mafi muhimmanci.
- Ko da cikin ba na halal babe kada kiyi yunkurin zubar da ciki, saboda kina iya rasa lafiyar ii ko ma ranki.
- Akwai hanyoyi da dama na kulawa da juna biyu – daga magani har zuwa shawarwari
Tambayoyi Da Amsoshi (FAQ)
1. Shin mace za ta iya jin alamar ciki tun satin farko?
Eh, wasu mata na jin sauye-sauye tun makon farko, musamman karamin ciwon mara ko sauyin nono.
2. Shin ana iya samun ciki kafin jinkirin al’ada?
Kwarai, ciki yana iya samuwa tun kafin mace ta samu jinkirin al’ada.
3. Ta yaya zan gane alamomin ciki ba su da alaÆ™a da al’ada?
Idan alamomin sun haɗa da gajiya, ciwon nono, ƙaiƙayi ko jin wari fiye da kima, yana iya zama alamar ciki.
4. Yaushe gwajin ciki zai fi tabbatar da sakamako mafi inganci?
Kwana 7 zuwa 10 bayan jinkirin al’ada shi ne mafi dacewa ayi gwajin ciki.
5. Shin alamomin ciki na farko suna kama da cututtuka?
Eh, amma bambanci zai bayyana ne idan alamomin suka wuce fiye da mako biyu.
Kammalawa
Alamomin shigar ciki a satin farko suna iya banbanta daga mace zuwa mace. Yayin da wasu ke jin sauyi nan take, wasu kuma ba sa jin komai sai bayan jinkirin al’ada. Abu mafi muhimmanci shi ne ki saurari jikin ki, ki dauki mataki da wuri, kuma ki nemi shawarar lafiya.
Idan kina da wata alama ko shakku, kar ki jira lokaci ya wuce kafin yin gwaji ko ganawa da likita.
Rubutu Masu Alaƙa
1. Yadda ake Zubar da Ciki a Nigeria: Dokokin Kasa da na Addinin Musulunci
2. Yadda Ake Gwajin Ciki A Gida: Wane Lokaci Ya Kamata Mace Tayi Gwajin Ciki Na Fitsari Da Tsinke?
3. Alamomin Shigar Ciki: Ya Mace Take Gane Tanada Ciki?
4. Matsanancin laulayi a farkon samun ciki da kuma yadda ake maganinsa (Hyperemesis gravidarum)
5. Ciwon Mara na Sha'awa – Sanin Abin da Ke Haddasa Shi da Hanyoyin Magancewa