Yadda ake Zubar da Ciki a Nigeria: Dokokin Kasa da na Addinin Musulunci

Assalamu alaikum warahmatullah. Yayana barka da safiya, ya aiki ya fama da jama'a? Muna godiya sosai da taimakon da kuke mana Allah ya biya ku. Yauma dai nazo da damuwata ne dakuma neman shawara. Dan Allah kada a gaji damu, banson yin posting a group saboda akwai wadanda suka sanni dayawa.

Dan Allah Yayana nayi family planning bayan haihuwata sai aka saka mini implant na 3 yrs to sai yake saka ni ramewa, naje nayi complain shine aka cire mini aka koma yi mun allura na wata 3. Toh ina kan wannan tsarin komai yana tafiya dai-dai, sai lokacin sallah allurar da akayi mini ya kare ni kuma sai naje gida sallah.

Dana dawo kuma ban samu naje na sake yin allurar ba har wajen two weeks amma fa mun hadu da mai gida na bayan dawowa ta, toh shi ne na fara jin canji a jiki na domin ko last month ko period dina ban gani ba, shi ne jiya naje nayi taste din ciki aka samu positive.

To ni dai yanzu wallahi ban shirya samun wani cikin ba nida mai gidana, domin yaron mu bai wuce 9 Month ba, shi kadai yaya nake karewa dashi wajen shayarwa balle kuma ga ciki kaga kuma akwai takura, toh a wajen da nake zuwa allurar nace musu bana bukatar cikin gaskiya sunce babu abunda zasu iya yi akai, nayi hakuri kawai.

Ni kuma gaskiya ban shirya ba, shine Dan Allah nake neman shawara a wajen ka Dr Dan Allah miye ya kamata nayi domin mijina Shima bai bukatar haihuwa yanzu. Cikin nawa bai wuce 4 to 5 weeks ba. Nagode Allah ya saka muku da alkhairi sai naji daga gare ka.

Amsa

To, ƙanwata, tunda kin riga kin tabbatar da ciki kuma ana iya kiyasin yana da makonni 4 zuwa 5, ba za'a yi magana a yanzu ba akan batun dakatar da cikin (abortion), domin wannan batu ya wuce matakin tunani, kuma ya shafi abubuwan da suka danganci doka, rayuwa, da addini.

Yadda ake zubar da ciki a Nigeria


Game da batun zubar da ciki da matsayin dokar ƙasarmu Nigeria, zubar da ciki ya sabawa doka, sai dai idan:

  • Rayuwar mahaifiya tana cikin hatsari kwarai
  • Kuma kwararren likita ne ya tabbatar da hakan bisa sakamakon binciken kimiyya na likitanci.

Dokokin Zubar da Ciki a Nigeria 

Dokokin da suke hana zubar da ciki a Najeriya sune:

  • Dokar Criminal Code Section 228–230 (Southern Nigeria) 
  • Dokar Penal Code Section 232 (Northern Nigeria)”. 

Dokokin suna haramta zubar da ciki ne, harma da tanadin hukunci mai tsanani ga likita da kuma maccen da aka zubarwa cikin. 

Dokar Criminal Code tace "wanda ya taimaka wajen zubar da ciki, ko kuma likitan da yayi aikin zubar da ciki ba a bisa ka'ida ba, za'a iya daure shi a kurkuku har na tsawon shekaru 14. Ita kuma macen da tayi yunƙurin zubar da cikin ta ba a bisa ka'ida ba, za'a iya ɗaure ta har na tsawon shekaru 7. 

Tabbas wannan shi ne dalilin da yasa ma'aikatan lafiya a asibiti suka ce miki babu abinda zasu iya yi miki. Idan kuma kika nace da cewa sai kinyi abortion kin zubar da cikin a hannun waɗanda ba ƙwararrun ma'aikatan lafiya ba, to, lallai zaki iya jefa kanki a cikin babban hatsari na rasa haihuwa nan gaba.

Ita kuma dokar Penal Code - Sashe na 232 (Northern Nigeria) tana goyon bayan tsarin Musulunci wanda ke haramta zubar da ciki ba tare da dalili mai karɓuwa ba (kamar ceton rai). Ma'ana, zubar da ciki yana iya haifar da hukunci mai tsanani. Dalili daga Al-Qur’ani:

 وَلَا تَقْتُلُوا أَوْلَادَكُم مِّنْ إِمْلَاقٍ ۖ نَّحْنُ نَرْزُقُهُمْ وَإِيَّاكُم ۚ إِنَّ قَتْلَهُمْ كَانَ خِطْئًا كَبِيرًا

Ma'ana: “Kada ku kashe ’ya’yanku saboda tsoron talauci. Mu ne muke azurta su da ku. Lallai kisan su babban kuskure ne.” (Surat Al-Isra’, aya ta 31). 

Sannan Hadisin Manzon Allah (SAW) yace:

 إِنَّ أَحَدَكُمْ يُجْمَعُ خَلْقُهُ فِي بَطْنِ أُمِّهِ أَرْبَعِينَ يَوْمًا، نُطْفَةً، ثُمَّ يَكُونُ عَلَقَةً مِثْلَ ذَلِكَ، ثُمَّ يَكُونُ مُضْغَةً مِثْلَ ذَلِكَ، ثُمَّ يُرْسَلُ إِلَيْهِ الْمَلَكُ، فَيَنْفُخُ فِيهِ الرُّوحَ...

Ma'ana: “Lallai ana tattara halittar ɗayan ku cikin mahaifiyarsa na kwanaki arba’in (40) a matsayin maniyyi, sai ya koma gudan jini, sai ya zamo tsoka, sa'annan sai a aiko da mala’ika ya hura masa rai...” (Hadisi ingantacce a cikin sahihaini).

Wannan yana nufin idan ciki, ya kai watanni 4, to, ya zamo mai rai kenan, don haka zubar da ciki a irin wannan lokaci yana daidai da yin kisan kai.

Kasashen da Suka Hana Zubar da Ciki 

Kasashen duniya da suka haramta zubar da ciki gaba daya, sune:

1. Nigeria

2. Senegal

3. Egypt

4. Angola

5. Madagascar

6. Honduras

7. El Salvador

8. Malta

9. Philippines

10. Dominican Republic

11. Nicaragua

12. Andorra


Haka zalika, 'yar uwata, kin bayyana cewa:

a. Ciki ya tabbatar yana da makonni 4 zuwa 5,

b. Kina da yaro ƙarami wanda kike shayarwa,

c. Kuna cikin rashin shiri, ke da mijinki, da ƙarancin ƙarfin tattalin arziki.

Dukkan wannan hakika wahala ce, amma ba kwakkwaran dalili bane a shari’a ko a dokar kasar mu ta Nigeria da zai halatta zubar da ciki. Wannan jarabawa ce da zata iya zamar miki kaffarar zunubai da tarin lada.

Abinda ya kamata kiyi yanzu 

Ki rungumi cikin da haƙuri da tawakkali

Ki fahimta cewa rayuwar wannan jariri daga Allah ce, kuma wataƙila shi ne mafi albarka a cikin 'ya'yanki baki daya, wanda zai iya zamo muku sanadiyyar buɗin kofofin arziki a gaba.

2. Ki kula da lafiyar ki

Ki fara zuwa asibiti wajen awo don a duba lafiyar cikin na ki da kuma na jaririn da kike shayarwa. Ki riƙa cin abinci mai kyau (kifi, ƙwai, kayan lambu, madara), tare da shan ruwa sosai. Ki riƙa samun isasshen hutu, idan akwai damar yin haka.

3. Ki dinga shayarwa tare da kula da juna biyu

Shayarwa da juna biyu suna iya tafiya lokaci guda idan aka kula da cin abubuwa masu gina jiki sosai. Ki tambayi likita don ya baki karin sinadarai (supplements) kamar folic acid, iron, da calcium domin jikin ki kada ya gaji.

4. Bayan haihuwa, ki zaɓi wani tsayayyen tsarin family planning da zai dace da lafiyar jikin ki: IUD, implant, ko wani nau’i da ya dace da lafiyarki shine a inda zaki yi amfani dashi. WalLahu A'lam.

Nassi

1. Amsa Tambayar: Dr. Usman Shehu Hassan a Facebook https://www.facebook.com/groups/785091171884812/posts/2358479524545961/

Rubutu Masu Alaƙa 

2. Yadda Mace Zata Dinga Yin Jarrabawa Ko Gwajin Nono A Gida Da Kanta 

3. Shin Mace Mai Ciki Na Iya Shan Maganin Duphaston, Folic acid, Dexamethasone, Navidoxine Ko Fanoclim?