Yaushe Zan Iya Samun Ciki Bayan Daina Amfani Da Hanyoyin Hana Haihuwa Da Tsarin Iyali?

Assalamu alaikum Dr. Na daina amfani da maganin hana haihuwa, yanzu kuma ina so in samu ciki. Don Allah tsawon wane lokacin da yake É—auka kafin jikina ya iya dawo da haihuwa?

Amsa

Daukar ciki bayan family planing

Lokacin da damar samun ciki ke iya dawowa mace bayan ta daina amfani da hanyoyin hana haihuwa ya danganta ne da irin hanyar hana haihuwa da aka yi amfani da ita. Zamu yi bayanin hanyoyin dalla-dallah a ƙasa;

1. Allurar hana daukar ciki 

Allurar Depo-Provera (Allurar tsarin iyali ta watanni 3) da allurar Noristerat (Allurar tsarin iyali ta watanni 2) su ne allurorin da aka fi amfani dasu domin hana haihuwa da bada tazarar iyali.

Shi irin wannan tsarin hana haihuwa ta hanyar yin allura yana iya jinkirta damar samun ciki har zuwa tsawon watanni 6 zuwa 12 daga ranar da aka yi allura ta ƙarshe. Wasu mata sukan iya daukar ciki da wuri bayan daina allurar, yayin da wasu sukan iya daukar sama da shekara ko fiye da haka kafin jikinsu ya dawo daidaita.

2. Implant (Implanon/Nexplanon/Jadelle)

Idan mace tana amfani da tsinken hannu na hana haihuwa, sannan daga baya ta bukaci haihuwa. Toh haihuwa na iya dawowa da gaggawa bayan an cire implant (tsinken) yawanci cikin makonni ko wata É—aya zuwa biyu. Wasu mata ma na iya yin ovulation cikin kwanaki kaÉ—an bayan cire tsinken.

3. Kwayoyin hana haihuwa

A mafi yawanci mace na iya daukar ciki a wata É—aya zuwa uku bayan ta daina shan Æ™wayoyin magani na hana daukar ciki da bada tazarar haihuwa. Wasu kuma sukan iya daukar har tsawon wata shida kafin jikin su ya daidaita da al’ada, amma ciki zai iya shiga tun kafin mace ta fara ganin jinin al'adar ta bayan ta dainanshan kwayoyin.

4. Patch, Ring, ko sauran hanyoyin hormonal

Su ma wadannan hanyoyin kamar hanyar shan kwayoyin magani ne, mafi yawancin mata na iya samun juna biyu cikin wata 1 zuwa watanni 3 bayan an daina amfani da su. Ko da jinin al’ada bai daidaita a lokacin ba, mace na iya yin ovulation kuma tana iya É—aukar ciki.

5. Na'urar Mahaifa (IUD)

Na'urar sanya wa a mahaifa domin bada tazarar iyali da hana haihuwa sun kasu kashi 2. Akwai na'urar cupper T wadda bata sake kowane irin sinadari, ita wannan mace na iya daukar ciki daga zarar an cire, ma'ana ana iya samun ciki tun a watan farko.

Akwai kuma na'urar roba wadda ke sake sinadaran hormones, ita wannan hukuncin ta É—aya ne da sauran hanyoyin hormonals.

Kammalawa

Kyakkyawan salon rayuwa kamar cin abinci mai kyau, rage tashin hankali, da kauracewa shan giya da tabar sigari na taimakawa saurin dawo da haihuwa bayan daina amfani da hanyoyin hana daukar ciki. Haka kum saurin dawowar haihuwa bayan yin planing ya danganta daga wata mace zuwa mace, shekarun mace da kuma lafiyar ta.

Lafiyayyin mata yan kasa da shekaru 35 a duniya sun fi saurin samun dawowar haihuwa bayan dainawa. Saboda haka, idan kun shafe shekara ɗaya kuna ƙoƙarin samun ciki amma ba tare da kunyi nasara ba, yana da kyau ku ziyarci likita da hanzari.


Rubutu Masu Alaqa 

2. Maganin Kara Girman Nono Da Man Shafawa Na Gyaran Nono: Hanyoyin Gyaran Nono A Likitanci

3. Bayani Game Da Cututtukan Nono (Breast Diseases)

4. Zubar Ruwan Nonon Mace Ba Tare Da Ciki Ko Shayarwa Ba (Galactorrhea)

5. Abubuwan Da Ke Kawo Kaikayin Nono Bayan Haihuwa