Aslm Dr ina da ciki 5 weeks Kuma likitana yace inada fibroid, kuma na taba miscarriage har sau biyu. Naje asibiti likita ya bani magunguna Duphaston, folic acid da para 1000 da cikina yakai 8 weeks watarana ina amai sai naji abu ya zubo a gabana, naduba Naga jini Sena koma asibiti likita yamin hoto yace komai lafiya lau. Daga nan ya ƙaramin magunguna navidozine dexa dakuma fanoclim. Toh Dr Yar uwata tazo tagani wai kar nasha idan nasha zasu wahalar dani wai harda na cutar Asma Dana the laulayi aciki dana ƙara kiba Dan Allah Dr ku karamin haske wlh tsoro nakeji nasha.
Duk magungunan da likita ya rubuta miki - Duphaston, Folic Acid, Paracetamol 1000mg, Navidoxine, Dexa, da Fanoclim - ana yin amfani dasu ne bisa takamaiman dalilai da kuma bayan yin bincike akan lafiyarki data cikinki. Misali:
- Duphaston yana taimakawa wajen tsare ciki idan akwai barazanar zubarwar cikin.
- Folic Acid yana taimakawa wajen girman kwakwalwar jariri da hana lahani a gareta da sauran sassan jikinsa.
- Navidoxine ana amfani dashi ne a wajen rage amai.
- Dexa (Dexamethasone) ana yin amfani dashi ne a wasu lokuta don rage kumburi ko matsalolin jini ko sinadaran jiki (hormones).
- Fanoclim yana da alaƙa da lafiyar ƙashi da hormones, kuma ba'a cika yin amfani dashi ba a lokacin juna biyu sai idan akwai dalili.
Ganin cewa kin taba miscarriage sau biyu, kuma kina da fibroid, likita zai iya rubuta miki wadannan magungunan bisa ga bukatar jikinki, amma ya kamata ya tabbatar da cewa baki da wata cutar numfashi, kamar asthma ko tari ko jini wadanda suke iya hana shan su. Idan ‘yar uwarki tana da irin wannan matsalolin, to magungunan ba lallai bane ke suyi miki illa.
Shawara anan ita ce idan kina da shakku ko tsoro, ki koma wajen likitan da ya rubuta magungunan ki shaida masa abinda ake ce miki, ya kara miki bayani da kwantar miki da hankalinki.
Kar ki daina shan maganin da likita ya rubuta miki saboda fargaba ko zancen mutane, sai dai idan wani likitan yai bincike akan lafiyarki kuma ya tabbatar miki da bukatar dainawa.
Amsa Tambayar; Dr. Usman Shehu Hassan
Rubutu Masu Alaqa
2. Maganin Kara Girman Nono Da Man Shafawa Na Gyaran Nono: Hanyoyin Gyaran Nono A Likitanci