Canker sore – wanda ake kira gyambon baki – wata ƙaramar kurji ce mai zafi da take fitowa a cikin baki. Yawanci tana fara bayyana ne da ɗan ƙaramin kurji mai radadi, wanda zai iya fitowa a harshe, gefen baki, cikin leɓɓa ko a saman ƙashin baki. Duk da cewa ba cuta ba ce mai hatsari a mafi yawan lokuta, tana iya jawo tsananin ciwo, wahalar cin abinci, shan ruwa ko ma magana.
A wannan rubutu, za mu yi cikakken bayani game da canker sore – mece ce, me ke haddasa ta, shin tana yaduwa ne ta mu’amala ko sumbata, da kuma hanyoyin magance ta cikin sauƙi da kuma lokacin da ya kamata a je asibiti.
Menene Canker Sore?
Canker sore ana kiranta da sunan kimiyya Aphthous ulcer. Ita ce kurji mai launin fari ko rawaya a tsakiyarta, sannan gefenta yana iya zama ja saboda kumburi da inflammation. Yawanci tana da siffar zobe ko cikakken wata, kuma tana fitowa ne a cikin baki – ba a saman leɓɓa ba.
⚠️ Kada a rikita ta da cold sore (herpes) wanda kwayar cutar virus ke kawowa kuma yana fitowa a waje ko gefen leɓɓa. Canker sore ba kwayar virus ke kawowa ta ba a mafi yawan lokuta.
Alamomin Canker Sore
Alamomin da aka fi gani sun haɗa da:
- Farin ko rawayar kurji a baki
- Ciwo mai tsanani musamman yayin cin abinci mai yaji ko tsami
- Wani lokaci gefen kurjin yana zama ja
- Jin ciwo ko ƙaiƙayi kafin ta fito
- A lokuta kaɗan, musamman ga yara, tana iya zuwa da zazzabi
Yawanci tana warkewa da kanta cikin kwanaki 7 zuwa 14. Amma akwai wasu masu tsanani da suke iya ɗaukar makonni uku ko fiye da haka.
Shin Canker Sore Tana Yaduwa Ta Mu’amala Ko Kiss?
A mafi yawan lokuta, canker sore ba ta yaduwa ta sumbata ko mu’amala. Ba cuta ce mai yaduwa kamar herpes ba.
Sai dai idan kurjin ta samu kamuwa da wata kwayar cuta ta daban (secondary infection), akwai yiwuwar yaduwa a yanayi na musamman. Amma gabaɗaya, ba cuta ce mai saurin yaduwa ba.
Me Ke Haddasa Canker Sore?
Har yanzu ba a gano takamaiman dalili guda ɗaya ba, amma masana sun gano abubuwa da dama da ke iya jawo ta:
1. Karancin Sinadaran Abinci
Rashin wadatar:
- Vitamin B12
- Folate (Vitamin B9)
- Zinc
- Iron
na iya sa jiki ya zama mai sauƙin kamuwa da gyambon baki.
2. Rauni a Baki
Cizon harshe ko cikin leɓɓa, ko amfani da burushin hakori mai kaifi, na iya jawo gyambo.
3. Allergy ko Mummunan martanin Garkuwar Jiki
Wasu lokuta garkuwar jiki na iya ɗaukar wani abu (abinci ko bakteriya) a matsayin barazana, ta haifar da kumburi da gyambo.
4. Sauyin Hormones
Wasu mata na fuskantar gyambon baki a lokacin al’ada saboda sauyin sinadaran hormones a jiki.
5. Yawan Damuwa (Stress)
Damuwa mai yawa na iya rage ƙarfi da daidaiton garkuwar jiki, wanda ke ba gyambo damar fitowa.
6. Kwayar Cutar H. pylori
Kwayar cutar Helicobacter pylori (H. pylori) wacce ake dangantawa da ciwon gyambon ciki (ulcer), ana ganin tana da alaƙa da fitowar canker sore a wasu mutane.
7. Wasu Cututtuka
Canker sore na iya zama alamar wasu manyan cututtuka kamar:
- Crohn's disease
- Ulcerative colitis
- Irritable bowel syndrome
- HIV
Idan gyambon baki na maimaituwa akai-akai ko yana da tsanani, yana da kyau a yi bincike domin a gano ko akwai wata cuta a bayan fage.
Nau’o’in Canker Sore
1. Minor aphthous ulcer – Ita ce mafi yawa. Tana da ƙanƙanta kuma tana warkewa cikin makonni biyu.
2. Major aphthous ulcer – Tana da girma kuma tana iya barin tabo.
3. Herpetiform ulcer – Ƙananan kuraje masu yawa da ke haɗuwa wuri guda a cikin baki.
Yadda Za A Magance Canker Sore A Gida
Idan gyambon bai yi tsanani ba, za a iya amfani da hanyoyin gida masu sauƙi:
1. Kurkure Baki Da Ruwan Gishiri
A sa cokali ɗaya na gishiri a cikin kofi ɗaya na ruwa mai ɗumi, a kurkure baki sau biyu a rana. Wannan yana taimakawa rage kumburi da kashe wasu kwayoyin cuta.
2. Kuskure Baki da Baking Soda (Bakin Soda)
A sa cokali ɗaya cikin ruwa mai ɗumi a kurkure a kalla sau uku a rana. Yana taimaka wa wajen daidaita acid a baki.
3. Shafa Zuma
Zuma mai kyau na da sinadaran rage kumburi da kashe bakteriya. A shafa sau 3–4 a rana.
4. Man Kwakwa
Yana da sinadaran antimicrobial. A shafa sau 3 zuwa 4 a rana.
5. Vitamin B Complex
Shan Vitamin B complex na iya taimaka wa masu fama da karancin vitamin.
Abubuwan Da Ya Kamata A Guje Su
Kada a shafa lemun tsami a kan gyambon baki – yana ƙara zafi da radadi.
Guji abinci mai yaji ko tsami.
Guji amfani da burushi mai kaifi ko wanda ya tsufa
A canja buroshin goge baki duk bayan 2-3 months
Lokacin Da Ya Kamata A Je Asibiti
- Ka garzaya asibiti idan:
- Gyambon ya wuce makonni biyu bai warke ba
- Yana da girma sosai
- Yana yawan maimaituwa ko fitowa
- Kana fama da zazzaɓi mai tsanani
- Kana da wata cuta kamar HIV ko cututtukan hanji
Likita na iya bada magungunan shafawa masu ɗauke da sinadaran steroid, ko maganin rage radadi, ko kuma ya ba da gwaje-gwaje domin gano dalilin.
Yadda Za A Kare Kai Daga Maimaituwar Canker Sore
- Cin abinci mai gina jiki
- Rage damuwa
- Amfani da burushi mai laushi
- Shan ruwa mai yawa
- Gujewa abinci da ke jawo maka allergy
Kammalawa
Canker sore (gyambon baki) ba cuta ce mai hatsari ba a mafi yawan lokuta, kuma yawanci tana warkewa da kanta cikin makonni biyu. Amma tana iya zama alamar wata matsala ta ciki ko rashin sinadaran gina jiki idan tana yawan maimaituwa.
Idan gyambon bai warke ba ko yana da tsanani, kar a yi sakaci – tuntubi likita domin a gano musabbabin matsalar. Lafiya ita ce jari. Idan ka kula da abinci, tsaftar baki da rage damuwa, za ka rage yiwuwar fuskantar wannan matsala.

No comments:
Post a Comment