Haihuwa wata abu ce da take barin alamomi a jikin mace. Ko da kuwa mace ta haihu da kanta (wanda ana iya samun dinki ko tsagewa) ko kuma ta hanyar aiki (C-Section), jikinta yana buƙatar kulawa ta musamman domin raunin ya warke ba tare da ya kawo matsala ba.
Ga matan da suka samu dinki ko rauni a gaban su yayin haihuwa, sirrin warkewa yana cikin abubuwa guda biyu: Tsafta da kula da gaban mace yadda ya kamata.
Amfani da ruwan ɗumi (ba mai zafi sosai ba) wajen tsarki bayan kowane bayan gida yana rage raɗadi da kashe ƙwayoyin cuta.
Bayan an wanke, kada a goge wurin da ƙarfi. A yi amfani da tsumma mai laushi ko takardar tishu (tissue paper) a matsa a hankali har ya tsane. Danshi shi ne abokin gaban kowane irin miki.
Ku Karanta: Alamomin sanyin mara da yadda ake maganin sanyin mara na mata(PID)
Idan mace tana samun damar kwanciya ba tare da audugar haihuwa ba na ɗan wani lokaci (lokacin da take hutu), hakan yana sa iska ta shiga raunin ya bushe da sauri.
Ga uwar da aka yi wa aiki Kuma (CS), rauninta yana saman ciki ne, kuma kulawar ta ɗan bambanta:
A guji ɗaukar nauyi ko yin ayyukan ƙarfi da suka shafi lanƙwasa jiki. Barin ciki ya huta shi ne babban magani.
Idan mace za ta yi tari, atishawa, ko dariya, hikima ita ce ta ɗaura matashi (pillow) a saman cikin ta matsa kaɗan. Hakan yana rage girgizar da za ta samu dinkin.
Sanya tufafi budaddu da kuma wadanda na nau'in auduga (cotton) waɗanda ba za su matse wurin dinkin ba.
Alamun Haɗari (Red Flags)
Dole ne ki zama mai lura da rauninki sosai. Idan aka ga ɗaya daga cikin waɗannan, zuwa asibiti shi ne mafita:
▪️Idan wurin dinkin ya yi ja sosai, ya kumbura, ko yana fitar da ruwa/ruɓa.
▪️Idan dinkin ya fara tsinkewa ko buɗewa.
▪️Idan wurin yana fitar da wari marar daɗi.
▪️Idan zafi da raɗadin wurin maimakon su ▪️ragu, sai ƙaruwa suke yi.
Kula da rauni ba kawai domin ado ba ne; domin kariya ce daga kamuwa da cututtukan da za su iya dakatar da uwa daga kula da jaririnta. Maigida ma, yana taka rawar gani wajen taimaka wa uwa da ayyukan da za su sa ba ta takura wa kanta ba, shi ne babban gatan da za a ba ta a wannan lokacin.
Tambayoyin da Aka Fi Yi (FAQ)
1. Yaushe raunin haihuwa ke warkewa?
Yawanci tsakanin makonni 2 zuwa 6, gwargwadon yadda aka kula da shi.
2. Shin ya dace mace ta yi wanka kullum bayan haihuwa?
Eh, tsafta na da matuƙar muhimmanci, amma a yi amfani da ruwan ɗumi.
3. Yaushe mace za ta fara aiki bayan C-section?
Yawanci bayan makonni 6, amma sai da shawarar likita.

No comments:
Post a Comment