Shan Nono Da Ciki: Shin akwai matsala mace ta cigaba da shayarwa bayan ta samu ciki?

Aslm shin dr mace na iya ci gaba da shayar da jaririn ta bayan tabbatar da samuwar juna biyu gareta

Amsa

Yadda ake shan nonon mace ma ciki

Mutane da yawa sun yi imanin cewa shayarwa a lokacin da mace ke dauke da ciki yana da illa ga yaron da ke shan nono, har wasu na ganin cewa duk yaron da yasha nono a lokacin da mamarsa ke da ciki toh zai yita cututtuka ba iyaka (wannan shi suke kira da shan ciki). 

Duk da haka, binciken masana ya tabbatar da cewa shayarwa a lokacin da mace keda ciki ba abu ne mai matsala ba gareta, cikinta ko jaririn da take shayarwa. 

Tsaraba: Abubuwan Dake Sa Namiji Jin Haushin Mace Bayan Saduwa 

Ruwan nono yakan samu canjin yanayi, dandano, yawan sinadarai da kuma iya yin ƙaranci a lokacin da mace ta samu ciki, amma duk da haka yana dauke da sinadarai masu gina jiki wadanda yaro ke bukata. Wannan canjin ruwan nono yana samo asali ne saboda canje-canjen sinadaran hormones da samun ciki ke haifarwa, kuma wannan canjin yanayin ruwan nono shi ke sa yaron ya daina jindadin ruwan nono, wani ma sai ya daina sha ya yaye kansa baki daya.

Yadda ake shan ciki


Mafi akasari kuma wannan yana faruwa ne kamin yaro ya saba da cin abincin gida. Toh a irin haka idan ba'a kula da yaro ba sosai, baya samun nonon da yake so, kuma baya samun ingantaccen abinci mai gina jiki sai yaro ya tsamure ya fara cututtuka daban daban wani ma daga nan sai tamowa ta ce masa Salamu Alaikum.

Shawara a nan shi ne: Idan an haihu ayi amfani da hanyoyin bada tazarar iyali har zuwa yaron da aka haifa yayi ƙwari yasha nono ya ƙoshi idan an yaye shi sai a cigaba da neman wani. Amma kuma idan an samu akasi an samu ciki ba tare da yaye yaro ba, to babu laifi a cigaba da shayarwa tare da samarwa yaro ƙarin ingantaccen abinci mai gina jiki da kula ta musamman.

No comments: