Idan ka tashi Aure kar kace kai lallai iya Genotype da HIV zaku yi, yanada matukar muhimmanci kuyi duk wani pre-marital test wanda ya kamata. Wasu suna gujewa kashe kuɗi sai su ce a musu iya Genotype da HIV test kawai, yin hakan akwai matsala musamman ga Mace koda baida complete kudi a hannun shi yakamata ki cika masa domin kusan status dinku.
Babbar barazanar rashin yin hakan akwai Blood Group a ciki, misali ka Aure Macen da Blood Group dinta 0-Negative kai kuma sai naka yazo 0+Positive baku sani ba. Wannan shine babban tashin hankalin da ake kira "Rhesus incompatibility".
Rubutu Mai Muhimmanci: Gwaje-gwajen da ya kamata ma'aurata suyi kamin su ƙulla niyyar aure (Premarital screening tests)
Barazanar da zaku fara fuskanta itace lokacin da Matarka ta samu ciki, Mace mai Blood Group O-Negative idan ta Aure Miji mai Positive kamar O+, A+, B+, ko AB+, akwai yuwuwar jaririn dake cikinta ya kasance mai Positive kamar mahaifinsa.
Inda matsalar take shi ne, ita Matarka Negative ce, idan yaron jinin shi ya zama Positive jikin uwarshi zai dauki jinin yaron a matsayin foreign object ma'ana bakon abu haka zai saka Anti-bodies din jikin Matarka su kaiwa jaririnta farmaki tun yana a ciki.
Kun san mi ye dalilin daya saka zaku ga wasu Matan suna samun yawan zubar ciki, suna yawan bari, suna yawon haifan yaro ba rai, suna yawan haifan yara da cutar shawara wanda ake kira da jaundice, ko a haifa yaron da zai dinga zama kusan ko wani lokaci da cutar karancin jini na Anemia?
Wannan matsalar ta Rhesus incompatibility tana daya da ga cikin manyan dalilai. Amma a mafi yawanci idan mace tana yawan fuskantar irin wannan matsalar idan har ba'a gano dalilin ba sai a dinga cewa Mayu ne suka Shanye mata jini, ko ace mayu ne suke kashe mata jarirai saboda yawan zubar da ciki da yawon haifan mataccen yara ko yaro mai dauke da Anemia ko jaundice.
Babban tashin hankalin na biyu a lokacin da Mace ta samu ciki shi ne, su mutane masu 0-Negative suna iya baiwa kowa jinin su amma su ba kowa bane yake iya basu jini sai mai irin nasu jinin na O- Negative shi yasa ake kiransu da Universal Donors.
Karanta Rubutu Mai Alaka: Meke Kawowa Jarirai Dorawar Jiki Da Idanu?
A cikin mutane 100% kaso 7-8% ne kacal masu kalar jini 0-Negative sai yasa samun jini mai Negative yake karanci musamman a lokacin gaggawa wanda hakan yake sanadiyar mutuwar mutane dayawa.
Samun lafiyar yaran mace mai jini 0-Negative a lokacin da ta haihu shi ne a dinga yi mata Allurar Anti-D (Rhogam) cikin awanni 24 a duk lokacin da ta haihu. Ita Anti-D ana yin ta ne saboda Anti-bodies din jikin Matarka kar su dinga kaiwa jaririn dake cikinta hari.
Babban kalubale na uku shi ne tsadar Allurar Anti-D, kudinta yana iya kaiwa 100k, 150k ya danganta da asibitin da ka kai Matarka kuma ana yin allurar duk lokacin da ta haihu. A lalace zaka ajiye 100k -150k iya kudin Allura kawai.
Bawai rashin yarda da kaddara bane kaucewa fadawa cikin wannan hadarin, shi kanshi addini ya karantar da cewa ku kauracewa kanku fadawa cikin matsala ko masifa. Ubangiji Allah ya bamu lafiya da abinda lafiyar zata ci. Amin

No comments:
Post a Comment