Sau da yawa a kan ji mutane idan suka ga yaron da kansa ya ɗan mole ko ya taɓe a gefe daya ko ya dan yi ƙeya cewa wai laifin ungozoman sa ce da ba ta daidaita kan jariri yadda ya kamata ba.
Sai dai, wannan magana ta yi hannun riga da binciken masana. Domin ƙoƙon kan jarirai an haɗashi ne da ƙasusuwa masu faɗi guda bakwai, waɗannan ƙasusuwa suna haɗewa su yi ƙarfi har su bayar da cikakkiyar siffar ƙoƙon kai a cikin watanni shida da haihuwar jariri.
Saboda haka, kan jarirai na iya canja siffa idan aka samu ƙarancin lura yayin raino musamman a watannin farko bayan haihuwa.
Me yake kawo kan jarirai ko yara molewa, taɓewa ko yin kusurwa daga ƙeya?
Daga cikin matsalolin da ke haddasa wannan matsala akwai matsalar nan da a ke cewa "Positional Plagiocephaly" a turancin likitoci.
Wannan matsalar siffar ƙoƙon kai tana faruwa ne sakamakon kwantar da jarirai a bayansu tsawon lokaci ba tare da ana jujjuya su ba. Sakamakon ƙoƙon kan jariarai bai gama yin ƙwari sosai ba, wannan ya sa ƙoƙon kansu ke da haɗarin yin kusurwa ko mole wa.
Daga cikin alamomin sun haɗa da:
1. Molewa, taɓewa ko kusurwar ƙoƙon kai daga ƙeya.
2. Bambancin kunnuwa; ta yadda idan aka kalli kan yaro ko jariri daga sama za a ga kunnen ɓarin da ke da matsala ya zarce gaba zuwa fuska fiye da na ɗaya ɓarin.
Wannan matsala an kasa ta zuwa : Mafi ƙaranci, matsakaiciya da kuma mafi tsanani.
Amma wannan matsala ba ta shafar aiki ko lafiyar ƙwaƙwalwa, sai dai matsalar siffar ƙoƙon ka kawai.
Abubuwan da ke kawo wannan matsala
Bayan kwantar da jarirai tsawon lokaci a bayansu ba tare da ana jujjuya su zuwa hagu, dama ko rib-da-ciki ba. Akwai ƙarin matsaloli kamar:
Ƙarancin ruwan mahaifa.
Ƙuncin ƙugu ko mahaifar uwa.
Ɗaukar cikin tagwaye, ko fiye da haka.
Ɗaurewar tsokokin gefen wuya da ke kawo noƙewar wuyan jariri zuwa gefe guda wato "muscular torticolis", da dai sauransu.
Yadda ake maganin matsalar molewar kan jariri
Abin yi shi ne da zarar an haifi jariri to lalle ne a dinga lura da yanayin kwanciyarsa.
Misali:
1. A riƙa juya shi daga kwanciyar rigingine zuwa kwanciyar gefe; wato hagu ko dama ta hanyar tokarewa da naɗaɗɗen tawul ko zani. Ko kuma kwanciyar rib-da-ciki, amma a yayin kwanciyar rib-da-ciki akwai buƙatar ƙara lura da kuma sanya ido sosai. Domin kada hancin jariri ya toshe ya hana shi numfashi.
2. A ɗinga canja gurbin kai da ƙafafu, misali, idan yanzu kan jariri yana Gabas ne, to sai a juya ya koma Yamma. Hakan nan daga Kudu zuwa Arewa.
3. A rage yawan lokacin da jarirai ke ɗauka a cikin kujerar raino ko keken raino.
4. A ɗinga jujjuya kai ko fuskar jariri daga wannan ɓari zuwa wannan ɓari.
Idan iyaye ko ungozomomi za su lura da waɗannan shawarwari za a rage afkuwar wannan matsala.
Sai dai, idan kan yaro ya wuce fiye da watanni uku bai koma daidai ba, to akwai buƙatar zuwa asibiti domin ganin kwararru idan har iyaye suna da damuwa kan siffar kan yaron su.
Idan kin lura jaririn ki baya son kallon ko juya kansa zuwa wani ɓangare, ko kuma idan aka yi ƙoƙarin juya fuskarsa zuwa wani ɓangare yana kukan ciwo, to akwai buƙatar ganin likitan fisiyo.

No comments:
Post a Comment