Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Bayani game da yadda maza da mata ke balaga da kuma sauyin halitta da ake samu bayan balaga (Puberty)

Gabatarwa:

Lokacin balaga lokacin ne da É—aukacin halittar É—an adam ta zahiri da ta baÉ—ini kan sauya daga halittar Æ™ananan yara zuwa ta manyan mutane. Wannan sauyin halitta ba abu ne da ke faruwa dare É—aya ba, yakan É—auki wani É—an lokaci da bazai kasa wasu yan shekaru ba. A cikin wannan lokaci yara suna buÆ™atar kulawa ta musamman daga wurin iyaye saboda akwai matsalolin da kan iya aukuwa da zasu shafi yadda  yara ke gudanar da rayuwar su har abada.

Yara manyan gobe 

Yaushe ƙananan yara ke fara balaga?

Ƙananan yara mata suna fara balaga ne a lokacin da suke tsakanin shekara takwas (8) zuwa shekara goma sha uku (13). Su kuma yara maza suna fara balaga ne a lokacin da suke tsakanin shekara tara (9) zuwa shekara goma sha huɗu (14). Wannan shi ne lafiyayyen wa'adin da mafi yawancin yara suke fara nuna alamomin balaga wanda likitoci masu ƙwarewa ta musamman a fannin kiwon lafiyar yara suka yarda dashi.

Yadda maza ke balaga

ƘwaÆ™walwa ita ce ke sarrafa dukkan gangar jikin É—an adam. Yayin da É—an adam ya kai mizanin balaga wane sashe na Æ™waÆ™walwar sa da ake kira da hypothalamus-pituitary-gonadal-axis ya kan yi umurni ta hanyar fitar da wasu sinadaran hormones da ake kire leutenizing hormone (LH) da follicle stimulating hormone (FSH) zuwa cikin jini. 

A maza, waÉ—annan sinadaran hormones na LH da FSH sukan yi umurni ga 'ya'yan marina (testes) da su fara fitar da wadatattun sinadaran hormones na androgens. Wadatuwar sinadaran androgens waÉ—anda Æ´aÆ´an marina ke Æ™irÆ™ira kuma su fitar da su a cikin jinin yaro matashi a yayin da ya fara balaga shi ne yake sanya duk wani chanji dake faruwa ga yaro a lokacin balaga. 

Waɗannan sinadaran hormones na androgens sune ke kula da sauya halittar yaro ƙarami zuwa baligin namiji, su ne ke kula da sha'awar namiji da kuma dukan abinda ya shafi harkokinsa na jima'i. Muhimman sinadaran hormones na androgens guda uku ne kamar haka:

  1. Testosterone
  2. Dihydrotestosterone
  3. Androstenedione
Ƙirƙirar wadannan sinadaran hormones na androgens yana ƙaruwa sosai a lokacin da yaro yakai mizanin shekarun balaga, wannan shi ne musabbabin duk wani sauyin yanayi da ake samu yayin balaga.

Yadda mata ke balaga

Idan É—iya mace ta kai mizanin balaga ita ma sashen Æ™waÆ™walwarta  da ake kira hypothalamus-pituitary-gonadal-axis yakan yi umurni ga ovaries É—inta domin su fara fitar da wadatattun sinadaran hormones na mata da ake kira estrogens da progesterones. WaÉ—annan sinadaran hormones sune ke sauya halittar su daga Æ™ananan yara zuwa 'yan mata.

Bugu da Æ™ari, waÉ—annan sinadaran hormones guda biyu su ke kula da sha'awar mace, yanayin jinin al'adar ta da kuma duk wasu harkokinta na jima'i. 

Glands ɗin ovaries da ke jikin mace su ke ƙirƙirar sinadaran estrogens da progesterones. Amma wani abin al'ajabi, su waɗannan glands na ovary suna fara ƙirƙirar sinadaran hormones na androgens ne sannan suyi amfani da wasu enzyme proteins da ake kira 3-BHSD da aromatase su maida androgens zuwa estrogens da progesterones. Wannan shi yasa za'a iya samun sinadaran hormones na androgens waɗanda ba'a maida estrogens ko progesterones ba a cikin jinin mace. Samun waɗannan sinadaran hormones na androgens dayawa a jinin mace shi yake sa mace ta siffantu da wasu siffofin maza, kamar babbar murya mai kauri, saje da kuma gashin baki.

Haka kuma shi ma namiji yana da waɗannan enzymes ɗin masu maida sinadaran hormones na androgens zuwa sinadaran mata na estrogens da progesterones (3BHSD da aromatase), amma enzymes ɗin basu da yawa. Samun waɗannan enzymes ɗin dayawa a jinin namiji shi yake sa namiji ya siffantu da wasu siffofin mata kamar irin su, ƙaramar murya, namiji ya fitar da nono, da sauran siffofin mata. Wannan yana faruwa ne saboda enzymes ɗin zasu maida mafi yawan sinadaran hormones na androgens zuwa sinadaran mata na estrogens da progesterones.

Yadda nono da gaban mace ke balaga


Alamomin balagar maza

Alamomin balagar maza suna fara bayyana ne ga Æ´aÆ´an marina (testes) da kuma fatar dake É—auke da su (scrotum).
  1. 'Ya'yan marina zasu ƙara girma
  2. Fara fitowar gashi a mara
  3. Fitowar gashi a fatar da ke ƙunshe da ƴaƴan marina
  4. Azzakari zai ƙara girma da kauri
  5. Azzakarin yaro zai kama miƙewa akai-akai, musamman idan yaro yana bacci.
  6. Fitar da ruwan maniyyi 
  7. Mafarkin jima'i tare da fitar da ruwan maniyyi
  8. Fitar gashi a ƙarƙashin hamata
  9. Fitar gashi a fuska; gemu, saje da gashin baki
  10. Muryar yaro zata ƙara kauri
  11. Wasu maza sukan samu fitar nono guda ko duka biyu, wanda daga baya zai zo ya É“ace bayan watanni 6 zuwa 18.
  12. Kafaɗar yaro zata ƙara girma ƙirjin sa ya buɗe.
  13. Jikin yaro zai ƙara girma sosai
  14. Yaro zai fara sha'awar mata da sha'awar yin jima'i.
Yadda gaban yaro yake girma zuwa na baligi

Alamomin balagar mata

Mafi yawancin mata farkon abinda ke fara nuna sun fara balaga shi ne fitar nono a ƙirjinsu. Fitar nono yana farawa ne da wani ƙaramin kumburi a ƙarƙashin kan nono, daga nan sai yaci gaba da girma. Sauran alamomin balaga sun haɗa da:
  1. Fitar da gashi a kumburin dinka ko kuma a manyan leɓɓan farji. (Labia majora).
  2. Fitar da gashin mara
  3. Fitar gashin hamata
  4. Fitar da nono
  5. Yanayin jikinsu zai sauya, kwankwasonsu (hips) zai ƙara girma ya buɗe, haka kuma za suyi manyan ɗuwawu
  6. Kitse zai taru a jikinsu, wannan zai ƙara musu girma da kuma laushin fata
  7. Fara yin jinin al'ada; mafi yawanci jinin al'ada ya kan fara ne bayan shekara É—aya ko biyu da fara fitar da nono.
  8. Siririyar murya; A lura cewa yayin da yarinya take farkon balaga muryar ta takan iya fara kauri kamar ta maza kamin ta koma siririya irin ta mata daga baya.
  9. Yawan fitar da ruwan maziyyi ko yawan jin danshi a farji.
  10. Sha'awar namiji ko sha'awar yin jima'i.


Sauyin hankali da tunani da ake samu bayan balaga


Ƙananan yara sukan samu ƙarin hankali, wayo da kuma zurfin tunani bayan sun balaga. Wannan shi ne zai taimaka musu domin daina wasu ɗabi'un yara da kuma shiga cikin manya. Kaɗan daga cikin abubuwan da ke faruwa sun haɗa da:
  1. Rage dogara da iyaye
  2. Ƙara kaifin basira da zurfin tunani
  3. Jin kunya
  4. Sanin ciwon kai
  5. Sanya tufafi yadda ya kamata
  6. Son sirri

Matsalolin da balaga ke iya kawo wa

  1. Warin jiki - Body odour
  2. Ƙurajen balaga - Acne
  3. Wasu yara sukan shiga yanayin ƙunci musamman mata sanadiyyar fitar da nono ko fara yin jinin al'ada
  4. Ciwon mara a lokacin jinin al'ada
  5. Sauyin yanayi - Mood changes
  6. Yawan fitar wani ruwa daga farji ko azzakari
  7. Sha'awar jima'i da zata iya sa yara lalacewa
  8. Yaro kan iya fara wasa da al'aurar sa - Masturbation
  9. Yin ƙiba ko taiɓa

Wane yaro ya kamata a kai asibiti idan yana cikin shekarun balaga

  1. Yaro namiji da ya fara nuna alamomin balaga kamin yakai shekara tara (9).
  2. Yarinyar da ta fara nuna alamomin balaga kamin ta kai shekara bakwai (7).
  3. Yarinyar da kai shekara goma sha uku (13) bata fara nuna alamomin balaga ba.
  4. Yarinyar da ta kai shekara biyar da fara fitar da nono amma bata fara jinin al'ada ba
  5. Yarinyar da ta kai shekaru goma sha shida (16) amma bata fara jinin al'ada ba.
  6. Yaro namiji da yakai shekara goma sha huÉ—u (14) amma ba fara nuna alamomin balaga ba.
  7. Yaro ko yarinyar da ke son a chanja musu jinsi - Gender dysphoria.
  8. Yaro ko yarinyar da suka fara shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.
  9. Yaro ko yarinyar da suka shiga halin ƙunci sakamakon fara bayyanar alamomin balaga.
  10. Yaro ko yarinyar da ta fara jima'i barkatai

Kammalawa

Lokacin balaga lokaci ne da yara ke buƙatar kulawa ta musamman da taimakon shawarwari daga wurin iyayensu. Yana da kyau iyaye su sa ido sosai a lokacin da yaran su ke cikin wannan lokacin balaga, domin lokaci ne da yara ke mallakar hankalin kansu, lokaci ne da suke fara sarrafa linzamin rayuwar su a matsayin cikakkun mutane.

Idan kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake Æ™asa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 

Nassoshi


Print this post

Post a Comment

0 Comments