Gwajin Ciwon Sukari: Yadda Ake Bayyana Sakamakon Gwajin Sukarin Jini

Ciwon sukari


Duk mai fama da ciwon sukari akwai buƙatar ya mallaki na'urar auna yawan sukarin jini ta kansa, wanda hakan mataki ne da zai bashi damar kula da adadin sukarin jinin sa a kowane hali da kuma gane lokacin da ya kamata ya nemi taimakon gaggawa.

Sakamakon awon sukarin jinin ya danganta da lokacin da aka yi ne. Za a iya fassara sakamakon kamar yadda zamu yi bayani a ƙasa, kuma yana da matukar muhimmanci duk mai ciwon sukari ko mai kula da ma ciwon sukari ya riƙe waɗannan lambobin saboda ya sauƙaƙa wa kansa wajen fassarar sakamakon awon sukarin jini a lokacin da ake yi a gida.

A duk lokacin da marar lafiya ya auna adadin sukarin jinin sa da na'urar gwajin sukarin jini da ake kira da glucometer, sakamakon gwajin ya kan zamo ne É—aya daga cikin waÉ—annan halaye gudu uku da zamu ambata kuma muyi bayani akan su.

  1. Hypoglycemia 
  2. Normoglycemia
  3. Hyperglycaemia 
A wasu lokuta zamu iya auna sukarin jinin mu amma na'urar auna sukarin jini ta nuna mana "Unrecordably Low" wannan yana nuna matsanancin karancin sukarin jini. Yana nuna cewa sukarin jini yayi ƙasa sosai ta yadda na'urar ba zata iya auna shi ba. Wannan yanayin hypoglycemia ne mai buƙatar taimakon gaggawa domin kaucewa hasarar rayuwa.

Haka zalika, wani lokaci lokaci zamu iya auna sukarin jinin mu, na'ura ta nuna mana "Unrecordably High" wannan yana nuna matsanancin hauhawar sukarin jini ta yadda na'urar ba zata iya kirga adadin sukarin da ke cikin jinin mu ba. Wannan wani yanayin hyperglycaemia ne dake buƙatar neman taimakon gaggawa a asibiti domin kaucewa hasarar rayuwa.

Hypoglycemia - Ƙarancin sukari a cikin jini

Wannan shi ne idan sukarin jini yayi Æ™asa da 70 mg/dL [3.9 mmol/L]. Wannan babban matsala ne, saboda haka duk wanda ya sami awon jinin sa Æ™asa da wannan sai ya yi hanzari ya sha abinda yake da sukari kaman lemun kwalba ko maltina, saboda ana da buÆ™atan sukarin jinin sa ya É—aga da sauri har ya kasance aÆ™alla 70 mg/dL [3.9 mmol/L] ko kuma sama da haka. 

Sannan kuma ana bukatar mutum ya sake gwada jinin na sa bayan ɗan lokaci da shan abinsha ko cin abin da zai daga sukarin jinin domin a sami tabbacin cewar sukarin jinin ya kai ƙimar da ya dace.

Normoglycemia - Lafiyayyen adadin sukari a cikin jini

Normoglycemia shi ne mu samo sakamakon gwajin sukarin jini da muka yi ya faÉ—o cikin lafiyayyen adadin da ake bukata na sukarin jinin É—aukacin al'umma. Lafiyayyen adadin da ake bukata na sukarin jini ya danganta da wane irin gwajin sukari akayi da kuma lokacin da aka yi gwajin sukarin.

I. Fasting blood glucose test (Gwajin sukarin jini da ake yi bayan mutum yayi azumin aƙalla awa 8)

Mafi yawanci ana yin wannan gwajin ne da safe kafin mutum yaci komai bayan ya shafe awa aÆ™alla 8 - 12 bai ci komai ba (bayan cin abincin dare da kaman 8 - 12 hr). Lafiyar wannan gwajin shi ne idan sukarin jini ya faÉ—o tsakanin 70 - 126 mg/dL [3.9 – 7 mmol/L].

II. Postprandial blood sugar test (Wannan shi ne awon sukarin jini da ake yi bayan cin abinci da wani ƙayyadadden lokaci)

1 hr after a meal (bayan cin abinci da awa É—aya kacal), lafiyar wannan awon shi ne ya faÉ—o a tsakanin 160 - 200 mg/dL [8.9 – 11.1 mmol/L].

2 hr after a meal (bayan cin abinci da awa biyu kacal): 140 - 180 mg/dL [7.8 – 10 mmol/L].

III. Random blood glucose test (a ko wani lokaci za'a iya yin wannan gwajin)

Wannan shi ne gwajin sukarin jini da ake yi ba tare da la'akari da mutum yaci abinci ko bai ci ba, ana iya yin wannan gwajin a kowane irin hali. Lafiyar wannan gwajin shi ne idan sakamakon ya faÉ—o a tsakanin 70mg/dl - 200 mg/dL [3.9mmol/L - 11.1 mmol/L].

Hyperglycemia - Hauhawar sukarin jini 

Wannan shi ne hauhawar sukarin jini fiye da Æ™imar lafiyayyen adadi. Ma'ana sama da 200 mg/dL [11.1 mmol/L]. Wannan ma matsala ce mai girma wanda yake nuni ga cewa sukarin jinin mutum ya wuce Æ™ima. Sukarin jini da ya wuce wannan Æ™ima, shi ma yana bukatar taimakon gaggawa amma bai kai matsalar hypoglycemia ba. 

A wannan halin, yakamata mutum ya nemi shawarar likita akan abinda ya kamata yayi domin ya sauko da awon sukarin jinin sa. Sannan kuma ya gwada jinin na sa bayan dan lokaci domin a samun tabbacin cewar sukarin jinin sa ya sauko ƙasa a daidai ƙimar da ta dace.

Wane Lokaci Ne Mafi Dacewar Yin Gwajin Sukarin Jini A Lokacin Azumi?

Zan ba da shawara da cewa a jira har sai lokacin Magrib ya gabato kafin ka yi awon sukarin jini. Ta wannan hanyar, zaka sami gamsashshiyar sakamakon da zai yi nuni a game da yanda sukarin jinin ka yake a yayin da ka ke yin azumi (fasting blood sugar). 

Duk da haka, yakamata mutum ya auna sukarin jinin sa a kowane lokaci yayin azumi duk sanda ya ji yunwa matsananciya ko kuma jiri, ko wasu alamomin Æ™arancin sukari a jini saboda gujewa saukar sukarin jini can Æ™asa sosai wanda zai haifar da hypoglycaemia. 

A kowane lokacin azumi idan har awon sukarin jinin ka ya zama yayi ƙasa sosai, to wajibi ne ka karya azumin ka a take ta hanyar cin abincin da zai daga maka sukarin jinin ka nan take ko da kuwa an kusa shan ruwa. Wannan yana da matukar muhimmanci, saboda shiga yanayin hypoglycemia kan iya salwantar da rayuwa.

Kwararru kan harkar kiwon lafiya suna yin gargadi cewa ƙarancin sukarin jini sosai ya fi muni akan hauhawar sukarin jini kuma ya kamata a nisanta daga faduwar sukarin jini sosai ta kowane hanya. Dafatar za'a kiyaye.

Domin kauce wa faduwar sukarin jini sosai a lokacin azumi, yana da kyau ka haÉ—a abincin sahur É—in ka yadda ba za ka ji yunwa ba sosai kafin shan ruwa, kamar haka: – 

Abinci maras sitaci sosai (misali tuwon oats/ acca/alkama (wanda ba a surfe ba), faten wake, da sauransu) + abinci mai furotin da yawa (dafaffen ƙwai 1 ko 2) + abinci mai maiƙo ko kitse (yogurt wanda yake tare da manshanu).

Idan ka bi wannan hanyar, da wuya ace ka fuskanci matsananciyar yunwa ko kuma jiri kafin shan ruwa. Har ila yau, yakamata mutum ya kula da cigaba da yin awon sukarin jinin sa a ko da yaushe ko da kuwa ya na yin amfani da irin wannan haÉ—in abincin da muka ba da shawara a sama don gujewa faduwar sukarin jini wanda zai iya haifar da yanayin gaggawa na hypoglycemia.


Rubutu Masu Alaqa

1. Abubuwan Da Ke Kawo Ciwon Sugar Da Alamominsa (Diabetes mellitus)

2. Cututtukan da ke sa mata yin gashin gemu, saje da gashin baki - (Hirsutism)

3. Illolin Ciwon Sugar Ga Mace Mai Ciki: Shin Ciwon Sugar Na Hana Haihuwa?

4. Taimakon Gaggawa Da Ya Kamata Kowa Ya Sani Don Ceto Rayuwar Masu Ciwon Sugar

5. Facts You Need To Know About Diabetes Mellitus: Symptoms, Causes, Types and Treatment