Illolin Hanyoyin Zubar Da Ciki Ga Lafiyar Mace Bayan Abortion

Gabatarwa

Zubar da ciki (abortion) wata hanya ce da ake amfani da ita a asibiti domin dakatar da rayuwar ciki kafin haihuwa. A wasu lokuta, ana yin wannan aiki bisa dalilai na asibiti, musamman idan lafiyar uwa tana cikin haÉ—ari ta dalilin wannan ciki. Amma a wasu lokutan kuma, ana yin shi saboda dalilai na zamantakewa, kamar zubar da ciki da aka samu ba ta hanyar aure ba, ko zubar da cikin da ba'a shirya É—aukar sa ba.

Duk da yake akwai bambancin ra’ayi tsakanin al’ummomi da addinai kan halalci ko haramcin zubar da ciki, abu daya ne tabbatacce: abortion yana da illoli masu yawa ga lafiyar mace, jikinta da ma tunaninta (mental health).

Illolin zubar da ciki

A cikin wannan rubutu, za mu yi bayani dalla-dalla kan side effects of abortion (illolin zubar da ciki), daga Illolin jiki zuwa na kwakwalwa, sannan mu tattauna hanyoyin kariya da yadda mace za ta kula da lafiyarta bayan ta samu abortion. Wannan bayani zai taimaka wajen wayar da kai musamman ga mata da ma mazajen da ke da alaka da su.

Illolin Zubar Da Ciki a Jikin Mace (Physical Side Effects of Abortion)

1. Zubar jini mai yawa

Daya daga cikin manyan illolin abortion shi ne zubar jini (bleeding). Bayan zubar da ciki ta hanyar amfani da maganin zubar da ciki na asibiti ko wasu hanyoyin zubar da ciki na asibiti ko na gargajiya, mace na iya fuskantar jini mai yawa wanda zai iya janyo matsalar karancin jini (anaemia) ko ma barazanar mutuwar mace idan zubar jinin ya yawaita kuma ba a samu kulawar likita ba.

Rubutu Mai Alaka: Yadda ake Zubar da Ciki a Nigeria: Dokokin Kasa da na Addinin Musulunci 

2. Rauni a Mahaifa (Uterine damage)

Lokacin da aka yi amfani da kayan aikin tiyata ko allura wajen zubar da ciki, ana iya lalata bangon mahaifa. Wannan lalacewa tana iya kawo matsalolin haihuwa a nan gaba, har ma ta janyo mace ta rasa damar samun ciki gaba daya.

3. Kamuwa da Kwayoyin Cuta (Infections)

Side effects of unsafe abortion sun haÉ—a da kamuwa da kwayoyin cuta idan aka yi aikin ba tare da tsafta ba ko kuma aka yi shi a wajen da bai dace ba. Wannan cutar na iya farawa daga cikin mahaifa ta bazu zuwa sauran sassan jiki kamar bututun haihuwa da ovaries.

Ku Karanta: Alamomin sanyin mara da yadda ake maganin sanyin mara na mata(PID) 

4. Raunin Bakin Mahaifa (Cervical injury)

Wani lokaci, lokacin cire dan tayin, ana iya janyo rauni a bakin mahaifa. Wannan na iya janyo matsalar budewar bakin mahaifa cikin sauki a nan gaba, wanda zai iya haddasawa mace matsalar budewar bakin mahaifa kamin ciki ya girma a nan gaba (cervical incompetence).

5. Rashin Zubewar Ciki Baki Daya 

Wasu lokuta, bayan abortion, ragowar sassan dan tayi na iya ci gaba da kasancewa a mahaifa. Wannan yana janyo ciwon ciki, zubar jini, da kuma kamuwa da cuta idan ba a gano da wuri ba.

6. Rashin Haihuwa (Infertility)

Idan aka yi abortion ba bisa ka’ida ba, akwai yiyuwar mace ta rasa damar samun ciki gaba daya. Wannan na faruwa ne saboda lalacewar mahaifa ko toshewar bututun haihuwa.

Ku Karanta: Yaushe Zan Iya Samun Ciki Bayan Daina Amfani Da Hanyoyin Hana Haihuwa Da Tsarin Iyali?

Illolin Zubar Da Ciki Ga Hankali da Tunanin Mace (Psychological Side Effects of Abortion)

1. Tashin hankali da Damuwa (Depression)

Yawancin mata da suka yi abortion suna fama da matsalar ciwon damuwa (depression). Wannan na faruwa ne saboda nadama, tunanin addini, ko kuma rashin shiri wajen daukar irin wannan mataki.

2. Zargin Kai da Nadama (Guilt and regret)

Daga cikin illolin abortion akwai jin laifi na dindindin. Wasu mata suna jin cewa sun aikata kuskuren da ba za a iya gyarawa ba, musamman idan suka rasa samun haihuwa a nan gaba.

3. Matsalolin bacci (Sleep problems)

Wasu mata sukan kasa samun isasshen bacci bayan abortion saboda tunanin da ke damunsu ko mafarkai masu tsoro. Wannan yana iya janyo karin matsalar lafiya a gaba.

4. Matsalar aure ko dangantaka

A lokuta da dama, abortion kan janyo matsaloli tsakanin mata da mazajensu ko abokan zamansu. Rashin fahimtar juna da nadama kan kawo sabani har ta kai ga rabuwa.

Illolin Zubar Da Ciki Da Ke Daukar Dogon Lokaci (Long-term Side Effects of Abortion)

1. Ciwon sanyin mahaifa (Pelvic Inflammatory Disease - PID): Wannan cuta ce da ke lalata mahaifa da bututun haihuwa, wacce kan kawo rashin haihuwa nan take.

2. Hadarin samun ciki a bayan mahaifa: Bayan abortion, mace na iya fuskantar daukar ciki a wajen mahaifa (ectopic pregnancy), wanda ke da matukar hadari.

Karin Bayani: Bayani Game Da Samun Ciki A Bayan Mahaifa - Ectopic pregnancy 

3. Ciwon mara da ciwon ciki mai tsanani: Wasu mata na fama da ciwon mara mai tsawo saboda lalacewar mahaifa.

4. Zubewar ciki haka kawai a nan gaba (recurrent miscarriages): Idan mahaifa ta lalace, mace na iya rasa damar rike ciki zuwa lokacin haihuwa.

Illolin Zubar Da Ciki na Al’ada da Addini

A yawancin al’ummomi, abortion abu ne da ake kallonsa da rashin mutunci ko sabawa addini. Wannan matsin lamba na al’umma kan kara wa mace damuwa da bakin ciki. A cikin addinin Musulunci, misali, zubar da ciki ba tare da Æ™wakkawaran dalili na gaggawa ba ana daukarsa babban laifi ne.

Yadda Za a Rage Illolin Abortion

1. Shawarwarin likita: Kafin a dauki matakin abortion, mace ta nemi shawara daga likita don sanin illolinsa.

2. Kulawa da mace bayan abortion: Idan aka riga aka yi, wajibi ne mace ta dinga zuwa duba lafiyarta akai-akai.

3. Kariya daga daukar ciki da ba a shirya ba: Yin amfani da hanyoyin family planning da hana daukar ciki zai rage yawan bukatar abortion.

4. Wayar da kan mata da al’umma: Ilimantar da mata kan illolin abortion da hanyoyin kariya zai rage yawan mace-macen da ke faruwa saboda zubar da ciki ba bisa ka’ida ba.

5. Saurin aurar da samari da yan mata: Saurin yin aure ga duk wanda Allah ya hore ma iko, zai rage yawan zina da É—aukar cikin da ba'a shirya ba.

Ku karanta: Illolin Maganin Zubar Da Ciki Ga Budurwa 

Kammalawa

Illolin zubar da ciki (side effects of abortion) suna da yawa kuma suna shafar lafiyar mace ta jiki da kwakwalwa. Zubar da ciki ba wai kawai yana iya janyo hadari ga mace a lokacin da aka yi shi ba, har ma yana iya yin tasiri a rayuwarta gaba daya.

Don haka, ya kamata mata su yi taka-tsantsan kafin daukar wannan mataki. Shawarar likita, ilimi kan lafiyar mata, da amfani da hanyoyin kariya daga daukar ciki (contraceptives) su ne manyan hanyoyin da za su taimaka wajen rage samun Illolin zubar da ciki.

A karshe, abu mafi muhimmanci shi ne kare lafiyar mace domin ita ce ginshikin al’umma. Abortion yana da illoli masu tsanani, kuma saninsu zai taimaka wajen yanke shawarar da ta dace da kare lafiyar mace da rayuwarta.

No comments: