Shin Rashin Kyakkyawan Ruwan Zai Iya Haddasa Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya?

Gabatarwa

Ruwa muhimmin ginshiƙi ne na rayuwa. Ba za a iya rayuwa ba tare da ruwa ba, domin yana da matuƙar muhimmanci ga lafiyar jiki, tsafta, noma, girki da sha. A Najeriya, musamman a yankunan karkara da wasu birane masu cunkoso, mutane da dama na amfani da ruwa marar tsafta daga rijiyoyi, koguna, rafuka ko rijiyoyin burtsatse (borehole) marasa inganci. Wannan matsala na haifar da manyan barazana ga lafiyar al’umma.

Illolin amfani da gurbataccin ruwa a Nigeria

Tambayar da mutane da yawa ke yi ita ce: shin rashin kyakkyawan ruwan sha na iya haddasa cututtuka masu yaduwa a Najeriya? Amsar ita ce eh, ƙwarai kuwa. Wannan rubutu zai yi cikakken bayani kan yadda gurbataccen ruwa ke haddasa cututtuka, irin cututtukan da ake kamuwa da su, dalilan da ke ƙara tsananta matsalar ruwa a Najeriya, da kuma hanyoyin kariya.

Rubutu Mai Alaka: Cututtukan da ke yaɗuwa ta hanyar amfani da gurɓataccen ruwa a Nigeria

Menene Ma’anar Rashin Kyakkyawan Ruwa?

Ruwa mara kyau shi ne ruwa da ya ƙunshi:

  • Kwayoyin cuta (bacteria)
  • Kwayoyin virus
  • Ƙwayoyin parasite
  • Guba daga sinadarai (chemicals)
  • Najasa daga kashin mutane ko dabbobi

Irin wannan ruwa ba ya dacewa da sha, girki ko wanka saboda yana iya haddasa cututtuka masu tsanani.

Yadda Rashin Kyakkyawan Ruwa Ke Haddasa Cututtuka Masu Yaduwa

Cututtuka masu yaduwa suna faruwa ne idan ƙwayoyin cuta sun shiga jikin mutum ta hanyoyi daban-daban. Ruwa mara tsafta na ɗaya daga cikin manyan hanyoyin shigar cuta a jiki. Ga yadda hakan ke faruwa:

  1. Sha ko amfani da ruwa mai dauke da najasa
  2. Wanke kayan abinci da gurbataccen ruwa
  3. Wanka da ruwa mai ɗauke da ƙwayoyin cuta
  4. Amfani da ruwa mara tsafta wajen wanke hannu ko kayan girki

Da zarar ƙwayoyin cuta sun shiga jiki, suna iya haddasa cututtuka masu yaduwa cikin sauri, musamman a wuraren da mutane ke zaune a cunkushe.

Cututtuka Masu Yaduwa Ta Hanyar Amfani da Gurbataccin Ruwa a Najeriya

1. Cutar Kwalara (Cholera)

Kwalara na daga cikin fitattun cututtukan da ruwa mara tsafta ke haddasawa a Najeriya. Ana kamuwa da ita ta hanyar shan ruwa ko cin abinci da ya gurɓata da ƙwayar cutar Vibrio cholerae.

Alamomin cutar kwalara sun haɗa da:

  • Zawo mai tsanani
  • Amai
  • Rashin ruwa a jiki
  • Gajiya mai tsanani

Kwalara na iya kashe mutum cikin sa’o’i idan ba a samu magani da wuri ba.

2. Zazzabin Typhoid (Typhoid Fever)

Zazzabin ciki na typhoid cuta ce da ake kamuwa da ita ta hanyar shan ruwa ko cin abinci da ke ɗauke da ƙwayar Salmonella typhi.

Alamomin zazzaɓin typhoid sun haɗa da:

  • Zazzabi mai ɗorewa
  • Ciwon kai
  • Ciwon ciki
  • Gudawa ko ƙurajen jiki 

A Najeriya, rashin tsaftar ruwa da abinci na ƙara yawan wannan cuta, musamman a tsakanin yara da matasa.

3. Gudawa (Diarrhea)

Gudawa na daga cikin manyan cututtukan da ke kashe yara ƙanana a Najeriya. Ruwa mara tsafta na taka rawa sosai wajen yaduwarta.

Illolinta sun haɗa da:

  • Rashin ruwa a jiki
  • Raguwar nauyi
  • Raunin jiki
  • Mutuwa idan ba a kula ba

4. Cututtukan Hepatitis A da E

Waɗannan cututtuka na shafar hanta kuma ana kamuwa da su ta hanyar shan ruwa ko cin abinci mai gurbata da najasa.

Alamomi:

  • Rawar jiki
  • Zazzabi
  • Rawar ido da fata
  • Gajiya

5. Cututtukan Tsutsotsi (Parasitic Infections)

Tsutsotsi irin su schistosomiasis da roundworms na yaduwa ta hanyar ruwa marar tsafta, musamman a yankunan karkara.

Dalilan Da Ke Sa Rashin Kyakkyawan Ruwa Ya Yi Kamari a Najeriya

1. Rashin Isasshen Ruwan Sha Mai Tsafta

Mutane da dama ba su da damar samun ruwan famfo mai tsafta, don haka suna dogaro da rijiyoyi ko koguna.

2. Talauci

Talauci na hana mutane samun hanyoyin tace ruwa ko siyan ruwan kwalba masu tsafta.

3. Rashin Ilimi Kan Tsaftar Ruwa

Wasu mutane ba su san illar shan ruwa mara tsafta ba, ko kuma ba su san hanyoyin tsabtace ruwa ba.

4. Gurbatar Muhalli

Zubar da shara, najasa da sinadarai cikin rafuka da koguna da hanyoyin ruwa kamar gota na ƙara gurbata ruwa.

Illar Rashin Kyakkyawan Ruwa Ga Lafiyar Al’umma

  1. Ƙaruwa cututtuka masu yaduwa ta hanyar ruwa
  2. Mutuwar yara da tsofaffi
  3. Ƙarin kuɗin magani
  4. Raguwar ƙarfin aiki
  5. Lalacewar tattalin arziki

Hanyoyin Kare Kai Daga Cututtukan Da Ruwa Mara Tsafta Ke Haddasawa

1. Tafasa Ruwa Kafin Sha

Tafasa ruwa na kashe yawancin ƙwayoyin cuta.

2. Amfani da Sinadaran Tace Ruwa

Ana iya amfani da sinadaran chlorine ko tacewa (water filters).

3. Wanke Hannu Akai-Akai

Musamman bayan gama bayan gida da kafin cin abinci.

4. Inganta Tsaftar Muhalli

Guje wa zubar da shara da najasa a kusa da tushen ruwa.

5. Wayar da Kai

Ilmantar da jama’a game da illar ruwa mara tsafta na da matuƙar muhimmanci.

Rubutu Mai Alaka: Gwaje-gwajen da ya kamata ma'aurata suyi kamin su ƙulla niyyar aure (Premarital screening tests)  

Rawar Gwamnati Da Al’umma

  1. Samar da ruwan sha mai tsafta
  2. Gyaran famfunan ruwa
  3. Gina bandaki masu tsafta
  4. Wayar da kai ta kafafen yada labarai

Kammalawa

A bayyane yake cewa rashin kyakkyawan ruwa na iya haddasa cututtuka masu yaduwa a Najeriya, kuma wannan matsala na da girma sosai. Kwalara, zazzabin ciki na typhoid, gudawa da sauran cututtuka na ci gaba da barazana ga lafiyar al’umma saboda amfani da ruwa mara tsafta.

Magance wannan matsala na bukatar haɗin kai tsakanin gwamnati, ƙungiyoyi masu zaman kansu da al’umma gaba ɗaya. Idan aka inganta samar da ruwan sha mai tsafta da wayar da kai, za a iya rage yawan cututtuka masu yaduwa tare da kare rayukan jama’a.

Read this Post in English: Can Poor Water Cause Infectious Diseases in Nigeria?

Tambayoyi da Amsoshi  (FAQ) Kan Ruwa Mara Kyau da Cututtuka a Najeriya

1. Shin ruwa mara tsafta na iya haddasa cututtuka masu yaduwa a Najeriya?

Eh, ruwa mara tsafta na iya haddasa cututtuka masu yaduwa a Najeriya. Sha ko amfani da ruwa da ya gurɓata da ƙwayoyin cuta na iya jawo kwalara, zazzabin ciki, gudawa, hepatitis da sauran cututtuka masu hatsari.

2. Wane irin cututtuka ruwa mara kyau ke iya haddasawa?

Ruwa mara kyau na haddasa cututtuka kamar kwalara, zazzabin ciki na typhoid (typhoid fever), gudawa, cututtukan hanta irin su hepatitis A da E, da kuma cututtukan tsutsotsi.

3. Ta yaya gurbataccen ruwa ke yada cututtuka?

Gurbataccen ruwa na yada cuta ta hanyar sha, girki, wanke kayan abinci, wanka, da kuma wanke hannu, inda ƙwayoyin cuta ke shiga jikin mutum cikin sauƙi.

4. Me yasa cutar kwalara ke yawaita a Najeriya?

Kwalara na yawaita ne saboda rashin ruwan sha mai tsafta, tsaftar muhalli mara kyau, da zubar da najasa a kusa da tushen ruwa.

5. Me ya sa zazzabin ciki (typhoid) ya yi yawa a Najeriya?

Zazzabin ciki ya yi yawa ne sakamakon shan ruwa mara tsafta, cin abinci da ya gurɓata, da rashin wanke hannu yadda ya kamata.

6. Shin ruwa mara tsafta na iya kashe yara?

Eh, ruwa mara tsafta na iya kashe yara ta hanyar gudawa mai tsanani wadda ke haddasa rashin ruwa a jiki idan ba a kula da wuri ba.

7. Ta yaya ruwa mara kyau ke shafar lafiyar al’umma a Najeriya?

Yana ƙara yawan cututtuka masu yaduwa, mutuwar yara da tsofaffi, kuɗin magani, da rage ƙarfin aiki da ci gaban tattalin arziki.

8. Wadanne alamomi ne ke nuna cututtukan da ruwa mara tsafta ke haddasawa?

Alamomi sun haɗa da gudawa, amai, zazzabi, ciwon ciki, gajiya, rashin ruwa a jiki, da rawar ido ko fata a wasu cututtuka.

9. Ta yaya jama’a za su kare kansu daga cututtukan ruwa mara tsafta?

Ana iya kare kai ta hanyar tafasa ruwa kafin sha, tace ruwa, wanke hannu akai-akai, tsaftace muhalli, da guje wa amfani da ruwa daga gurɓatattun wurare.

10. Shin ruwan burtsatse (borehole) koyaushe yana da aminci?

A’a, ba kowane ruwan burtsatse ba ne ke da aminci. Idan yana kusa da rijiyar najasa ko ba a gwada shi ba, yana iya samar da gurɓataccin ruwa.

11. Wace rawa tsaftar muhalli ke takawa wajen yaduwar cututtuka?

Rashin tsaftar muhalli na sa najasa da shara su gurɓata ruwa, wanda ke ƙara yaduwar cututtuka masu yaduwa.

12. Shin tafasa ruwa na hana cututtuka?

Eh, tafasa ruwa na kashe yawancin ƙwayoyin cuta kuma hanya ce mai sauƙi da araha don kare lafiya daga cututtuka.

13. Me yasa har yanzu samun ruwan sha mai tsafta ke da wahala a Najeriya?

Dalilai sun haɗa da talauci, ƙarancin kayan more rayuwa, yawan jama’a, lalacewar muhalli, da rashin kulawar gwamnati a wasu yankuna.

14. Shin yankunan karkara sun fi fuskantar matsalar cututtukan ruwa mara tsafta?

Eh, yankunan karkara sun fi fuskantar matsalar saboda dogaro da koguna, rafuka da rijiyoyi, tare da ƙarancin wayar da kai kan tsafta.

15. Me gwamnati za ta iya yi don rage cututtukan da ruwa mara tsafta ke haddasawa?

Gwamnati na iya samar da ruwan sha mai tsafta, gina bandaki, wayar da kai, da kuma sa ido kan tsaftar muhalli da ingancin ruwa.

No comments: